Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sabon Babin Tsaro A Najeriya: Gombe Ta Fito Da Tsarin Smart Security Na Farko
Published: June 10, 2026 at 5:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Jihar Gombe ta sake kafa tarihi a fannin tsaro, bayan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda Mataimakinsa Dakta Manassah Daniel Jatau ya wakilta, ya kaddamar da wata cibiyar tsaro ta dijital ta zamani, tare da sabon ofishin ’yan sanda da gidajen kwana na zamani ga jami’an tsaro.

An gudanar da wannan muhimmin bikin ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Shalkwatar Gombe da ke kan titin Fadar Sarkin Gombe, a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026.

Wannan aiki, wanda aka bayyana a matsayin na farko irinsa a Najeriya, ya fito ne daga haɗin gwiwa tsakanin Galaxy Backbone, Asusun Tallafawa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (Nigeria Police Trust Fund), da Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya, domin inganta tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani da na’urorin sa ido na dijital.

Jami’ai sun bayyana cewa sabon tsarin zai taimaka wajen gano laifuka cikin gaggawa, hana aikata su tun kafin su faru, da kuma inganta martani ga matsalolin tsaro ta hanyar amfani da fasahar zamani da ke bin ƙa’idojin aikin ’yan sanda na duniya.

A gefe guda kuma, an gina sabbin gidajen kwana guda hudu na jami’an ’yan sanda masu ƙananan mukamai, domin inganta walwala da ƙara ingancin aikin jami’an tsaro a jihar.

Da suke zantawa da manema labarai, Shugaban PCRC na jihar, Comrade Garba Ubale, da Sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Saleh Danburam, sun yaba da wannan ci gaba, suna cewa zai ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ’yan sanda da al’umma, tare da inganta tsaron jama’a.

Haka kuma, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Gombe, CP Ahmed Chuso, ya samu yabo bisa jajircewa da ƙoƙari wajen kyautata alaƙar rundunar da jama’a da kuma inganta ayyukan tsaro.

Wannan mataki ya jawo hankalin masu bibiyar lamuran tsaro a ciki da wajen Najeriya, inda ake ganin Gombe na zama ɗaya daga cikin jihohin da ke jagorantar amfani da fasahar zamani wajen tabbatar da tsaro mai ɗorewa.

Afrika, Kimiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Iran: Za A Gudanar Da Jana’izar Khamenei Bayan Kwanaki Goma Na Muharram
Next Post: ’Yar Kasuwa Ta Tsallake Rijiya Da Baya Bayan Hari Da Saurayinta Ya Kai Mata

Karin Labarai Masu Alaka

NLC Ta Yabawa Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Najeriya
Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela Labarai
Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Haramtawa Amurkawa Shiga Kasashen Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya Afrika
  • Afirka Ta Kudu Da Kenya Sun Bayyana Yaudarar ‘Yan Kasashe Da Yawa Tare Da Sakasu Yaki Labarai
  • Yawan wadanda suka mutu a mummunan harin yanbindiga a Jihar kwaran Najeriya yakai 170 Najeriya
  • Shugaba Tinubu Yakarawa Mambobin ASUU Kashi 40 Na Albashi Najeriya
  • Amurka Zata Tantance Fararen Fata ‘Yan Afirka Ta Kudu Afrika
  • Hukumomin Bada Agaji Sun Fadakar Da Al’ummar Jihar Gombe Afrika
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Sarkin Kagarko Ya Rasu Yana Da Shekaru 110 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.