Shugaban Ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce ya kadu da labarin rasuwar tsohon jami’in sojin, wanda ya yi wa ƙasa hidima na tsawon shekaru kafin ya yi ritaya.
Shugaban ƙasar ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, musamman ga matarsa da har yanzu take hannun masu garkuwa da mutanen.
Haka kuma, ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Katsina da rundunar sojojin Najeriya bisa wannan babban rashi.
Tinubu ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta taɓa amincewa da buƙatar ’yan ta’adda ta sakin wasu daga cikin mambobinsu da hukumomin tsaro ke tsare da su ba.
Ya tunatar da kalamansa da ya yi a ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, inda ya yi kira ga ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Najeriya.
A cewarsa, “A matsayinmu na ’yan Najeriya, dole ne mu kasance cikin haɗin kai tare da tabbatar wa kanmu cewa makiyan ƙasa za su zama tarihi nan gaba kaɗan. Za mu yi nasara a kan ta’addanci tare da ci gaba da gina ƙasa mai ci gaba da wadata.”
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa rasuwar Janar Abubakar ya kamata ta zama wani muhimmin darasi a yaƙin da ake yi da ta’addanci da masu tayar da ƙayar baya, yana mai cewa bai kamata gwamnati ta shiga wata tattaunawa ko sulhu da su ba, domin su ne manyan maƙiyan ƙasar da ya wajaba a ci gaba da murƙushewa.


