Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ Afrika
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika

Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran
Published: July 3, 2026 at 7:54 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Za a fara gudanar da jana’izar Jagoran Ƙolin Iran da aka ce ya rasu sakamakon hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a farkon yaƙin.

Za a fara bukukuwan jana’izar ne a ƙarshen mako a Tehran, sannan a ci gaba da jerin gwanon jana’izar a mako mai zuwa a biranen Qom da Mashhad, tare da wasu bukukuwa a ƙasar Iraki.

Limamin sallar Juma’a na birnin Qom, Ayatollah Mohammad Saidi, ya shaida wa kafafen yaɗa labaran gwamnati cewa dimbin mutanen da za su halarci jana’izar zai zama wata alama ta goyon bayan Jamhuriyar Musulunci.

Rahotanni sun ce gwamnatin Iran na shirin tattara miliyoyin magoya baya daga sassa daban-daban na ƙasar, tare da samar musu da sufuri, masauki da abinci, domin nuna ƙarfin gwamnati bayan yaƙin da ta bayyana a matsayin babban ƙalubale ga wanzuwarta.

Haka kuma, rahotanni sun ce mutuwar jagoran da kuma maye gurbinsa da ɗansa, Mojtaba Khamenei, a matsayin Jagoran Ƙoli na uku na Jamhuriyar Musulunci, na daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa a tarihin ƙasar cikin shekaru 47 da suka gabata.

An kuma ruwaito cewa Mojtaba ya samu munanan raunuka a harin da ya kashe mahaifinsa, kuma tun bayan fara yaƙin ba a sake ganinsa a bainar jama’a ba.

Sai dai wasu masana na cewa, duk da ƙoƙarin gwamnati na nuna haɗin kai, akwai alamun cewa wasu daga cikin al’ummar Iran na ci gaba da nuna rashin gamsuwa da halin matsin tattalin arziki, takunkuman ƙasashen waje da kuma salon mulkin ƙasar.

Wata mazauniyar Tehran mai suna Samira, mai shekaru 35, ta ce ita da iyalanta ba sa shirin halartar jana’izar, kuma sun bar birnin domin kauce wa cunkoso da tsauraran matakan tsaro.

Afrika, Amurka, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa

Karin Labarai Masu Alaka

Dan Gudun Hijira Tarique Rahman Ya Kusa Zama Shugaban Kasa Labarai
Gwamnatin Gombe Ta Kaddamar Da Sabon Ofishin GOGIS Don Inganta Tsarin Filaye Afrika
Amurka Tana Cigaba Da Kare Jami’in Da Ya Kashe Ba Amurke Amurka
Yajin Aikin Ma’aikatan Lafiya Na Shafar Harkokin Jinya A Asibitoci Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano Ta Rufe Gidajen Bukukuwa Da Shakatawa Labarai
Hukumar Hisbah Ta Kona Barasar Dubban Nairori A Katsina Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jana’izar Jagoran Ƙolin Iran Ta Kawo Tsauraran Matakan Tsaro A Tehran
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki
  • Sojoji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Sun Ceto Mutane 1,516 – DHQ
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
  • Wasu Muhimman Abubuwa Da Najeriya Ba Zata Manta Da Su Ba A 2025 Labarai
  • Mayakan RSF Sun Zafafa Kai Hare Hare Da Jirgi Maras Matuki A Sudan Labarai
  • Gwamnatin Somaliya Da MDD Sun Bayyana Cewa Kimanin Mutane Miliyan Shida Da Rabi Suna Fuskantar Barazanar Yunwa Labarai
  • Baba Malam Ya Lallasa Abokan Hamayya Da Kuri’u Sama Da Dubu 236 A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Atiku Ya Zargi Gwamnati Da Kama ‘Yan Adawa Labarai
  • Shugaban Hukumar NAHCON Ya Yabawa ‘Yan Jarida Kiwon Lafiya
  • Isra’ila Takai Sabon Hari Tehran Ranar Lahadi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.