Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sarakunan Gombe Da Zazzau Sun Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Su Rungumi Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
Published: July 8, 2026 at 9:14 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na III, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su ƙara haɗa kai domin inganta haɗin kan ƙasa, zaman lafiya, tsaro da kuma kare al’adun gargajiya.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya.

Ya bayyana cewa ƙarfafa hulɗa da haɗin gwiwa tsakanin masarautun gargajiya na da matuƙar muhimmanci wajen magance ƙalubalen da ke barazana ga haɗin kan ƙasa da kuma ci gaban al’ummomi.


Ya ce ziyarar ta kasance ne domin ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙar da ta daɗe tsakanin Masarautun Gombe da Zazzau.

“Ba wannan ne karon farko da muka haɗu ba. Manufar wannan ziyara ita ce ƙarfafa ‘yan’uwantaka, haɗin kai da kuma zumunci tsakanin masarautunmu,” in ji Sarkin Gombe.
Sarkin ya ƙara da cewa ci gaba da tattaunawa da shawarwari tsakanin sarakunan gargajiya zai taimaka wajen bunƙasa zaman lafiya, inganta tsaro, kare ɗimbin al’adun Najeriya da kuma ƙarfafa haɗin kan al’umma.

Haka kuma, ya yabawa jagorancin Sarkin Zazzau, yana mai cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa gwamnati wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya tsakanin al’umma.
Da yake mayar da martani, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce ziyarar ta sake tabbatar da ɗorewar alaƙar da ke tsakanin masarautun gargajiyar Najeriya tare da nuna ƙudurin su na haɗa kan ƙasa.

Ya bayyana cewa dangantakar tarihi tsakanin Masarautun Zazzau da Gombe ta samo asali tun daga ƙarni na 19, a lokacin juyin juya halin Musulunci na Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, wanda ya bunƙasa shugabanci nagari, ilimi da zaman lafiya a Arewacin Najeriya.

Sarkin Zazzau ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi haɗin kai da haƙuri da juna, yana mai jaddada cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da jajircewa wajen inganta zaman lafiya, ilimi, ci gaban al’umma da haɗin kan ƙasa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gombe Ta Yi Kira Ga Jami’o’i Su Tallafa Wa Gwamnati Ta Hanyar Bincike Da Ƙirƙire-ƙirƙire
Next Post: Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci

Karin Labarai Masu Alaka

An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya Labarai
‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga ADC Afrika
Harin Ukraine Yayi Mummunan Barna A Rasha Afrika
Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
Wani Abu Ya Fashe A Ofishin Jakadancin Amurka Dake Kasar Norway Afrika
Rikici Ya Lafa A Kasar Iran Bayan Daukar Matakai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
  • Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika
  • Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
  • Shugaban Amurka Zai Sake Gine Gaza Amurka
  • Dakarun Zaman Lafiya Na Majalisar Dinkin Duniya Sun Rasa Rayukan Su Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Jirgi Marar Matuki Yayi Ajalin A Kallah Mambobin M23 9 Tare Da Kashe Kakakin Rundunar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.