Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro
Published: July 8, 2026 at 2:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun ƙaddamar da Kwamitin Amintattu na Asusun Tsaron Arewacin Najeriya (Northern Nigeria Security Trust Fund), inda suka bayyana matakin a matsayin wani muhimmin yunƙuri na ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da samar da ingantaccen tallafi.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya bayyana hakan yayin taron ƙungiyar da kuma ƙaddamar da kwamitin a ranar Laraba a Kaduna.

 

Ya ce an kafa Asusun Tsaron ne domin ya kasance mai taimaka wa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya wajen magance matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifuffuka da ke barazana ga rayuka, dukiyoyi da ci gaban tattalin arzikin Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa asusun zai kasance wata hanya ta tattara kuɗaɗe, ƙarfafa musayar bayanan sirri, inganta haɗin gwiwar hukumomin tsaro da kuma tallafa wa ayyukan tsaro a tsakanin jihohin Arewa da hukumomin tsaro na tarayya.

Ya ƙara da cewa an zaɓi mambobin Kwamitin Amintattu ne daga jihohin Arewa bisa ƙwarewa da nagarta, kuma ana sa ran za su tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ingantaccen gudanar da kuɗaɗen asusun tare da tsara ayyukan da za su inganta tsaro a yankin.

Muhammadu Inuwa Yahaya ya jaddada cewa bai kamata asusun ya zama wata sabuwar cibiyar gudanarwa da ke gudanar da taruka kawai ba, sai dai ya kasance wata kafa da za ta samar da sakamako mai ma’ana wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya tunatar da cewa tun a baya Gwamnonin Arewa sun amince kowace jiha tare da ƙananan hukumominta za su rika bayar da naira biliyan ɗaya duk wata na tsawon watanni 12 domin tallafa wa asusun. Ya yabawa jihohin da suka fara cika alƙawarinsu tare da kira ga sauran jihohi su gaggauta biyan gudummawar da suka ɗauka.

Gwamnan ya kuma sake bayyana goyon bayan Gwamnonin Arewa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya wajen dawo da zaman lafiya a ƙasar, tare da nuna goyon baya ga tattaunawar da ake yi kan kafa ‘yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsarin tsaro.

Haka kuma ya jaddada buƙatar magance tushen matsalolin tsaro ta hanyar zuba jari a fannonin ilimi, noma, samar da ayyukan yi, ƙarfafa matasa da koyar da sana’o’i, yana mai cewa matakan tsaro kaɗai ba za su wadatar wajen kawo ƙarshen matsalar ba.

Ya yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, shugabannin al’umma, ƙungiyoyin fararen hula, masu zaman kansu da abokan hulɗar ci gaba da su mara wa wannan shiri baya, yana mai cewa tabbatar da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana kwarin gwiwar cewa idan aka haɗa kai tare da nuna jajircewa da cika alƙawura, Asusun Tsaron Arewacin Najeriya zai taimaka wajen inganta haɗin gwiwar tsaro da samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa a yankin Arewa.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci
Next Post: Yayale Ahmed Ya Jagoranci Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaron Arewa

Karin Labarai Masu Alaka

Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
Farashin Danyen Mai A Amurka Ya Tashi Afrika
‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Afrika
Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika
  • Shugaban Amurka Yayi Watsi Da Tattaunawar Kawo Karshen Yaki Da Iran Afrika
  • Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
  • Za’a Fuskanci Bala’in Yunwa A Najeriya Labarai
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
  • Kasar India Ta Sayi Iskar Gas Daga Iran Labarai
  • Amurka Da Iran Sun Tattauna A Kasar Pakistan Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.