Makarantar Firamare ta Herwagana ta lashe kofin gasar ƙwallon ƙafa ta makarantun firamare da aka shirya domin bikin cika shekaru 100 da kafuwar Makarantar Firamare ta Hassan Central da ke Gombe.
An gudanar da wasan ƙarshe na gasar a Filin Wasan Pantami, inda Herwagana ta doke Hassan Central da ci 4–3 ta hanyar bugun fenariti bayan kammala wasa mai cike da gasa da nuna ƙwarewar matasan ‘yan wasa.

Shugaban gidauniyar Gombe Grassroots Movement, Alhaji Ahmed Shuaibu Gara Gombe, wanda shi ne jagoran shirya bukukuwan cikar makarantar shekaru 100, ya ce gasar ƙwallon ƙafar da ta guje-guje na daga cikin jerin shirye-shiryen da aka tsara domin tunawa da tarihin makarantar da kuma ƙarfafa ci gaban ilimi da wasanni a matakin firamare.
Ya bayyana cewa manufar gasar ita ce gano hazikan ‘yan wasa tun suna ƙanana, inganta zamantakewa tsakanin ɗalibai, da kuma amfani da wasanni a matsayin hanyar ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da gina kyawawan halaye.
Alhaji Gara ya ƙara da cewa bukukuwan cikar makarantar shekaru 100 za su ci gaba da wasu muhimman shirye-shirye, da suka haɗa da gabatar da laccoci a Jami’ar jihar Gombe kan tarihin Hassan Central da gudunmawar da makarantar ta bayar wajen bunƙasa ilimi, babban taron tsofaffin ɗalibai a harabar makarantar, da kuma karrama fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa wajen ci gabanta.
Ya yabawa kwamitin shirya bukukuwan, malamai, ɗalibai, iyaye, baƙi da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da goyon bayan da suka bayar, yana mai cewa hakan ne ya tabbatar da nasarar gudanar da gasar.

A jawabansu daban-daban, Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Alhaji Saifullahi Auwal, da Mataimakin Shugaban Gombe South LCDA, Alhaji Dalhatu Boderi, sun yabawa masu shirya gasar, suna mai cewa irin waɗannan shirye-shirye na taimakawa wajen bunƙasa baiwar yara, ƙarfafa haɗin kai da kuma inganta zaman lafiya tsakanin ɗalibai.
Sun kuma tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke bunƙasa ilimi da wasanni a matakin ƙasa.

Shi ma da yake nasa jawabin, Sakataren Ilimi na Ƙaramar Hukumar Gombe, Alhaji Abdullahi Baba, da Shugaban Kungiyar Malamai ta NUT Dalhatu Baba Ali sun buƙaci sauran makarantun firamare su riƙa shiga irin waɗannan gasa domin ba da damar gano da haɓaka ƙwararrun ‘yan wasa tun daga tushe.
Sunce, baya ga nasarar da ake samu a fagen wasanni, irin waɗannan gasa na ƙara wa yara ƙarfin guiwa, koyar da su aiki tare da kuma inganta tarbiyya da shugabanci.
Bukukuwan cika shekaru 100 da kafuwar Makarantar Hassan Central na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake gudanarwa a fannin ilimi a jihar Gombe a bana.
Ana sa ran za su haɗa tsofaffin ɗalibai, malamai, jami’an gwamnati, masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki domin waiwayar tarihin makarantar, nuna irin gudunmawar da ta bayar cikin ƙarni guda, da kuma tsara hanyoyin ci gaba da inganta ilimi ga al’ummomi masu zuwa.



