Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

NDPHC Ta Yi Alkawarin Tallafa Wa Gombe Wajen Inganta Wutar Lantarki
Published: August 14, 2026 at 10:06 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta jihar Gombe (GoSERC), tare da sauran Kwamishinoni biyar na hukumar, sun gana da Daraktan Gudanarwa mai kula da Hanyoyin Rarraba Wutar Lantarki na Kamfanin Niger Delta Power Holding Company (NDPHC), Injiniya Bello Babayo Bello, da Daraktan Gudanarwa mai kula da Harkokin Shari’a, Dr. Steven Andzenge, a ofisoshinsu da ke Abuja a Najeriya

Ganawar ta kasance wani bangare na ziyarar aiki da hukumar GoSERC ta kai, domin lalubo hanyoyin tabbatar da samar da wutar lantarki mai dorewa da kuma inganta ayyukan samar da wutar lantarki a jihar Gombe.

Taron ya mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi kula da harkokin wutar lantarki, da dabarun inganta samar da wutar lantarki da kuma yadda za a inganta ayyukan da ake bai wa al’ummar jihar.

Jami’an NDPHC din biyu sun bayyana aniyarsu ta yin hadin gwiwa da GoSERC wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma tallafa wa ci gaba mai dorewa a fannin wutar lantarki a jihar Gombe.

Sun kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki wajen magance kalubalen da ke addabar bangaren wutar lantarki, da kuma inganta samun ingantacciyar wutar lantarki mai dorewa ga al’ummar Jihar Gombe.

Ya kamata a tuna cewa gwamnatin jihar Gombe ta kafa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar Gombe (GoSERC) domin karfafa ikon jihar na tsara da kuma sa ido kan harkokin wutar lantarki, tare da tallafa wa aiwatar da sauye-sauyen kasuwar wutar lantarki a matakin jiha.

NDPHC ta yaba wa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa nada kwararru masu kwarewa da jajircewa wajen tafiyar da harkokin hukumar, musamman wadanda ke da masaniya kan samar da wutar lantarki da sauye-sauyen da ake samu a fannin.

Kamfanin ya bayyana kwarin gwiwar cewa jihar Gombe za ta kasance cikin jihohin da za su yi takara da sauran jihohin Najeriya wajen jawo jarin da zai bunkasa bangaren wutar lantarki da sauran harkokin ci gaba.

NDPHC ta kuma yi alkawarin ba jihar Gombe dukkan goyon bayan da ake bukata domin cimma manufofinta na inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa jarin da ake zubawa a fannin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Pads To Prosperity: NEDC Ta Horar Da Mata 280 Kan Kera Pads A Gombe
Next Post: Malaman Tsangaya A Gombe Sun Goyi Bayan Inuwa Yahaya Da Jamilu Gwamna

Karin Labarai Masu Alaka

Wani Jami’in Iran Yace Amurka Taso Kanta A Tattaunawar Tsagaita Wuta Amurka
Amurka Ta Girke Jirage Marasa Matuki Tare Da Sojoji A Najeriya Afrika
Jagoran Addinin Kirista A Kaduna Ya Rabawa Fiye Da Musulmai Dubu Kayan Abincin Azumi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
Dogarawan Ruwa Na Amurka Suna Yunkurin Shiga Wani jirgin Dakon Mai Da Aka Allakan Ta Da Venezuela Labarai
An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
  • Amurka Ta Jefa Makamin Tomahawk A Makarantar Yara Mata Afrika
  • Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
  • Gombe Ta Ƙaddamar da Allurar Rigakafin HIV Ta LEN PrEP Afrika
  • REAL MADRID: VALVERDE YA SAMU RAUNI MAI TSANANI A ƘAFA Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasashe 5 Da Ke Fama Da Matsanancin Zazzabin Cizon Sauro Rediyo
  • Shugaban Al’ummar Igbo Ya Buƙaci Karfafa Noma domin Tabbatar Da Wadataccen Abinci Afrika
  • Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.