Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Pads To Prosperity: NEDC Ta Horar Da Mata 280 Kan Kera Pads A Gombe
Published: August 14, 2026 at 8:02 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar Raya Arewa maso Gabashin Najeriya (NEDC) ta yi alkawarin ci gaba da sanya ido da kuma tallafa wa mata 280 da suka samu horo a karkashin shirin “Pads to Prosperity Community Pad-Making Enterprise Programme” a Jihar Gombe.

Mai Kula da ayyukan NEDC a Jihar Gombe, Architect Usman Muhammad, ne ya bayyana hakan a wajen bikin rufe shirin horaswar da aka gudanar a Gombe.

Ya ce hukumar ta himmatu wajen inganta rayuwar al’ummar yankin Arewa maso Gabas ta hanyar samar da shirye-shiryen da za su bunkasa kwarewa, samar da ayyukan yi da kuma dogaro da kai.

Architect Usman ya yaba wa mahalarta shirin bisa jajircewa da hadin kan da suka nuna a lokacin horaswar, inda ya bayyana cewa an zabo mahalarta daga kananan hukumomin Dukku, Funakaye, Gombe da Yamaltu Deba a matsayin wuraren gwajin shirin.

Ya bukaci wadanda suka amfana da horon da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen kafa kananan sana’o’i da za su taimaka wajen inganta rayuwarsu da ta al’ummominsu.

Shi ma da yake magana, Rufai Lawan Baba Manu, ya ce za a rika bibiyar shirin na tsawon watanni shida tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, domin tabbatar da cewa mahalarta sun samu damar mayar da kwarewar da suka koya zuwa sana’o’i masu dorewa.

Ya ce shirin na da manufar gina lafiya, samar da arziki da sauya rayuwar al’umma, musamman ta hanyar bai wa mata damar samun sana’a da dogaro da kai.

Rufai Baba Manu ya kuma yaba wa mahalarta bisa kyakkyawan hali, jajircewa da ladabtarwa da suka nuna, tare da tabbatar musu da cewa NEDC za ta ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai.

A sakonnin fatan alheri, Hajiya Fatima Umar Abubakar daga Ma’aikatar Harkokin Mata ta jihar Gombe, Dr. Gazali Abdulhamid, Shugaban kwalejin Ilimi ta Tarayya a Gombe, Malam Ibrahim Yusuf na kungiyoyin farar hula, da Hajiya Maimuna Abubakar ta Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), Gombe, da sauran masu ruwa da tsaki, sun yaba wa NEDC kan kokarin da take yi wajen sauya rayuwar al’umma ta hanyar samar da sana’o’i da dabarun dogaro da kai.

Sun ce irin wadannan shirye-shirye na taimakawa wajen rage radadin matsin tattalin arziki da samar da hanyoyin samun kudin shiga ga iyalai.

Sun kuma bukaci wadanda suka kammala horon da su zama masu horas da wasu (Training of Trainers), domin su yada ilimin da suka samu ga matasa da sauran al’umma, musamman a yankunansu.

Shirin Pads to Prosperity wanda NEDC ta dauki nauyin gudanarwa, tare da hadin gwiwar Virtuous Reusable Pads, ya mayar da hankali kan inganta lafiyar mata, samar da arziki da kuma sauya al’umma ta hanyar koyar da sana’ar kera kayan tsaftar mata da bunkasa kananan sana’o’i.

Afrika, Kimiya, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: CP Chuso Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Gwiwar Hukumomin Tsaro A Gombe
Next Post: NDPHC Ta Yi Alkawarin Tallafa Wa Gombe Wajen Inganta Wutar Lantarki

Karin Labarai Masu Alaka

Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
CAF Ta Hukunta Samuel Eto’o AFCON 2025 Labarai
Sakamakon Yakin Gabas Ta Tsakiya Kowacce Gangar Mai Ta Haura Dala 100 Afrika
Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan Labarai
Kamfanin Magani Na Aspen Yayi Gagarumar Asara A Cinikayya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji Afrika
  • Hukumar MDD Tace Wadanda Suka Mutu A Harin Sudan Sun Haura 70 Afrika
  • Zanga-Zangar Adawa Da Harin Amurka Da Isra’ila Ya Zamo Tarzoma A Pakistani Afrika
  • Za’a Gurfanar Da Sojojin Da Ake Zargi Da Yunkurin Juyin Mulki Najeriya
  • Iran Ta Tasa Keyar Wani Jirgi Shake Da Mai Sauran Duniya
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.