Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika
  • Kannywood: Ali Nuhu Ya Shiga Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu Afrika

Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
Published: August 22, 2026 at 7:57 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Tsohon Gwamnan jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya ce har yanzu yana cikin jam’iyyar APC, yana kuma tuntubar masu ruwa da tsaki kan makomar siyasarsa.

Goje ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a gidansa da ke Pantami, Gombe, lokacin da magoya bayansa da abokan siyasa suka kai masa ziyara.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rade-radin cewa tsohon gwamnan na fuskantar matsin lamba daga magoya bayansa da ke son ya sake neman kujerar Sanata a zaben 2027, bayan da bai samu tikitin APC a zaɓen fidda gwani na Sanatan Gombe ta Tsakiya ba.

Duk da rahotannin da ke cewa jam’iyyar PDP na matsa masa ya koma cikinta, Goje ya bayyana karara cewa bai sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba.

Ya ce, “Ban sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba. Har yanzu ina cikin APC,” sannan ya bukaci magoya bayansa su ci gaba da haɗin kai, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na siyasa hadin kai da biyayya.

Sai dai tsohon gwamnan ya bar kofar sake neman kujerar Sanata a bude, inda ya bayyana cewa tun farko bai shirya sake tsayawa takara ba, amma matsin lambar magoya bayansa na sa shi sake tunani.

Goje ya ce ya shafe shekaru 45 yana harkokin siyasa, inda ya rike mukamai daban-daban a matakin jiha da kasa, ciki har da shugabancin Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa.

Ya jagoranci jihar Gombe a matsayin gwamna na tsawon wa’adi biyu daga shekarar 2003 zuwa 2011, sannan ya zama Sanatan Gombe ta Tsakiya tun shekarar 2011.

An sake zabar Goje a matsayin Sanata a shekarun 2015, 2019 da 2023, abin da ke nufin idan ya sake tsayawa takara a 2027, zai kasance neman wa’adi na biyar a Majalisar Dattawa.

A zaben fidda gwani na APC da aka gudanar a watan Mayun 2026, Mohammed Ahmed, tsohon Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda, ya samu tikitin jam’iyyar na Gombe ta Tsakiya.

Sai dai Goje ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin, inda ya bayyana shi a matsayin na bogi tare da cewa za a fitar da sahihin sakamako a Abuja. Daga bisani, ba a samu sunansa cikin jerin ‘yan takarar Majalisar Dokoki ta Kasa da APC ta mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ba.

Wannan ci gaba ya kara haifar da rade-radin cewa Goje na iya neman kujerar Gombe ta Tsakiya a karkashin wata jam’iyya.

Rahotanni sun kuma nuna cewa PDP da African Democratic Congress, ADC, na zawarcin tsohon gwamnan, yayin da ake alakanta yiwuwar komawarsa PDP da batun neman kujerar Sanata da kuma goyon bayan dan takarar gwamnan jihar na PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Sai dai PDP ta riga ta tsayar da Aliyu Hammadu a matsayin dan takararta na Sanatan Gombe ta Tsakiya, lamarin da zai iya haifar da sauye-sauye a cikin tsarin jam’iyyar idan Goje ya yanke shawarar neman tikitin.

A nasa bangaren, Goje ya jaddada muhimmancin biyayya da hadin kai tsakanin magoya bayansa, yana mai cewa ya kamata ‘yan siyasa su hada kai domin cimma manufofin da suka dace.

Ya kuma bayyana cewa tasirinsa a siyasar jihar ya wuce jam’iyyar APC, inda ya ce ya horar da ‘yan siyasa daga manyan jam’iyyun siyasa daban-daban a Gombe a tsawon shekarun da ya shafe yana siyasa.

Ya ce, “Mutane daga dukkanin manyan jam’iyyun siyasa a jihar Gombe sun kasance wadanda na yi wa jagoranci a siyasa.”

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Shirye-Shirye, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028
Next Post: Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
Rundunar Sojin Amurka Sunfara Ficewa Daga Kasar Sham Amurka
Mizanin Tattalin Arzikin Najeriya Na 2024 Ya Karu Da Kashi 3.84% Labarai
Hamas Ta Mika Ma Isra’ila Gawar Daya Daga Cikin Mutane Biyu Sauran Duniya
Wani Jirgin Kasa Yayi Hatsari A Kudancin Spain Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Miliyan Biyar Ko Rayuwata: Barazanar ’Yan Ta’adda Ta Jefa Wani Mazaunin Dukku Cikin Fargaba Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Za’a Bude Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Ta Duniya 2026 Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Ware Kudade Domin Bunkasa Rayuwar ‘Yan Najeriya Afrika
  • Harin Bom Din Maiduguri Ya Kashe Mutane Biyar Ya Raunata Fiye Da Talatin Najeriya
  • An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya Afrika
  • Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • ‘Yan Sandan Gombe Sun Fara Kama Motocin Da Ba Su Da Lambar Rajista ko Masu Boye Lambobinsu Afrika
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.