Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya Afrika
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba Afrika

Miliyan Biyar Ko Rayuwata: Barazanar ’Yan Ta’adda Ta Jefa Wani Mazaunin Dukku Cikin Fargaba
Published: August 18, 2026 at 4:13 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Alhaji Musa Gurya wanda mazaunin kauyen Malala ne da ke karamar hukumar Dukku a jihar Gombe ya bayyana cewa rayuwarsa ta na cikin hatsari bayan wasu ‘yan ta’adda sun kai farmaki gidansu su ka kashe kaninsa amma shi Allah ya kubutar da shi bayan sun bi shi don kashe shi amma ba su samu nasara.

Musa Gurya ya ce a lokacin ‘yan ta’addan sun dauke wayoyin salularsu 4 da babur dinsa sabo da ya saya “a daren karfe 1:30am na kira DPO na Dukku na shaida ma sa abun da ya faru kuma shi da kansa ya zo a ka dauki gawar kanina tare da shi zuwa Malala inda mu ka yi ma sa jana’iza.”

Alhaji Musa ya cigaba da cewa bayan wata daya da aukuwar akasin sai barayin su ka sake kiran sa su na ma sa barazana ko ya ba su kudi Naira miliyan 5 ko su kashe shi.

Hakanan dai ya yi ta musayar magana da su. Gurya ya ce ya kai rahoto wajen DPO na Dukku inda a ka bi wayar da barayin ke aiki da ita inda a ka samu kama daya daga cikinsu mai suna Dauda. DPO ya tura batun zuwa CID “na kasha kimanin Naira miliyan 5 kan batun amma rana tsaka na ji an sake Dauda ba tare da zuwa kotu ba”

Alhaji Musa Gurya ya yi zargin da cewa da alamu su Dauda sun ba da wani kasafi ne a ka kyale su. Kazalika Gurya ya ce kwamshinan ‘yan sanda na Gombe ya na da masaniya kan akasin.

“Gaskiya ni da sauran ‘yan uwana mu na cikin tashin hankali ba ma iya barci da ido biyu.”

A Kokarin da mukayi Saboda Jin tabakin Jami’in Hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandar jihar Gombe DSP Buhari Abdullahi yaci Tura, inda ya bayyana cewa Suna Gudanar da bincike Akan lamarin.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: KADCCAM Ta Yaba Da Shuka Bishiyoyi A Kaduna
Next Post: An Yi Barazanar Kaurace Wa Gasar Cin Kofin Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Barau Jibril: Mu Ba ‘Yan Amshin Shata Bane A Majalisa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
INEC Mayar Da Lokacin Zaɓen 2027 Kafin Azumi Najeriya
An Samu Nasarar Karbo Karin Yara 130 Daga Hannun ‘Yan-Ta’adda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Shugaban Kasar Ghana Ya Soki Manufofin Gwamnatin Amurka Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • IMC Kaduna Ta Buƙaci Jama’a Su Fifita Haɗin Kai Da Zaman Lafiya
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel
  • Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki
  • Majalisar Malaman Yarbawa Ta Yi Jimamin Rasuwar Babban Limamin Nuruddeen A Gombe
  • ‘Yan Sanda Sun Haramta Amfani Da Drones Ba Tare Da Izinin NCAA Ba

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sanata Goje Yayi Watsi Da Fidda ‘Yan Takarar APC A Gombe Afrika
  • Iran Tana Duba Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Amurka Afrika
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
  • Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
  • Osun: Adeleke Ya Doke Oyebamiji, Ya Ci Gaba Da Rike Kujerar Gwamna Afrika
  • Jamhuriyar Nijar Ta Dakatar Da Bawa Amurkawa Visa Afrika
  • Shugaba Trump Ya Yabawa Iran Bisa Bude Mashigar Hormuz Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.