Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnonin Arewa Sun Yi Jimamin Rasuwar Sarakunan Gumel Da Zurmi
Published: September 3, 2026 at 5:20 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnonin Arewa, karkashin jagorancin Shugaban Northern Nigeria Governors’ Forum (NNGF) kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, sun mika sakon ta’aziyya ga al’ummar Jihohin Jigawa da Zamfara bisa rasuwar Sarakunan Gumel da Zurmi.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga Jihar Jigawa, Arewa da Najeriya baki daya.

Ya ce marigayin ya kasance basarake mai mutunci, wanda zamaninsa ya kasance cike da hikima, tawali’u, kokarin samar da zaman lafiya da kuma jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummarsa.

Gwamnan ya bayyana cewa Sarkin Gumel ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Masarautar Gumel, inda ya bar tarihi da za a ci gaba da tunawa da shi.

A cikin sakon ta’aziyyar da ya fitar a madadin gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya ya jajanta wa iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Gumel, al’ummar masarautar da kuma Gwamnati da al’ummar Jihar Jigawa.

Ya bukaci iyalan marigayin da al’ummar masarautar su samu kwanciyar hankali ta hanyar tunawa da kyawawan halaye da gadon da ya bari, musamman zaman lafiya, hadin kai, hidima ga al’umma da ci gaba.

Haka kuma, Shugaban NNGF din ya bayyana alhini kan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zurmi na Jihar Zamfara, Alhaji Bello Sulaiman.

Inuwa Yahaya ya bayyana marigayin a matsayin basarake mai mutunci kuma mai kishin al’ummarsa, wanda ya sadaukar da shekaru biyar da ya yi kan karagar mulki wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da jin dadin jama’ar masarautar.

Ya ce rasuwar Sarkin Zurmi babban rashi ne ga Masarautar Zurmi, Jihar Zamfara da kuma daukacin tsarin sarautun gargajiya na Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Zurmi, al’ummar masarautar da Gwamnati da al’ummar Jihar Zamfara, yana mai kira da su samu karfin guiwa daga kyawawan ayyuka da tarihin da marigayin ya bari.

Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa sarakunan biyu kura-kuransu, Ya karbi kyawawan ayyukansu, Ya sanya su cikin rahamarSa, Ya kuma ba su Aljannatul Firdaus.

Rasuwar Sarkin Zurmi ta faru ne a ranar Litinin, bayan shekaru biyar da hawansa karagar mulki.

Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gidauniyar Sultan Ta Jaddada Muhimmancin Kula Da Lafiyar Yara A Gombe
Next Post: RSF Ta Nemi A Gaggauta Gano Dan Jarida Moussa Kaka Da Ya Bace A Yamai

Karin Labarai Masu Alaka

Amurka Ta Kakaba Takunkumi Ga Kwamandojin Yakin Kasar Sudan Sauran Duniya
Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Hadakar Ta Da Amurka Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda Najeriya
2025 Ta Bar Baya Da Abubuwa Masu Ban Al’ajabi, 2026 Barka Da Zuwa! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura Labarai
  • Boko Haram Ta Kai Hari Maiduguri Cikin Dare Afrika
  • Wakilan Rasha Da Ukraine Sun Tattauna A Abu Dhabi Ranar Juma’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakai Don Farfaɗo Da Maɗaba’ar Gwamnati Labarai
  • Amurka Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Fara Wata Tattaunawa Afrika
  • Ferfesa Pantami Yasamu Tikitin Takarar Gwamnan Gombe A Jami’yar PDP Afrika
  • APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.