Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero
Published: April 19, 2026 at 4:00 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da ginin sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai karfin megawat daya (1MW) a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), domin kawo karshen matsalar duhu da tsadar makamashi da ke addabar jami’ar.

Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN), Dokta Mustapha Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan yayin taron kaddamar da aikin da aka gudanar a cikin jami’ar.

Dokta Abdullahi ya bayyana cewa wannan aiki ya zo da wata sabuwar fasaha ta musamman wadda ko kura ta yi yawa ko kuma hadari ya rufe rana, na’urorin za su ci gaba da bayar da wuta. Haka kuma, akwai tsarin sanya ido ta kwamfuta ko wayar salula domin sanin yadda wutar ke gudana.

“Wannan ba wai kawai sanya fanoni (panels) ba ne; tsari ne da aka hada shi da inbata (inverters), batura da tirasfoma wadanda ke aiki tare cikin tsari daya,” in ji shi.

Ya kara da cewa an riga an kawo muhimman kayayyaki kamar batura na ‘Lithium’ da fanonin hasken rana zuwa jami’ar, kuma an riga an amince da kudaden aikin, don haka ’yan kwangila za su shiga aiki gadan-gadan.

Wannan sabon aiki na zuwa ne daidai lokacin da ake kokarin farfado da wata tsohuwar tashar hasken rana mai karfin 3.5MW wadda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya kaddamar a shekarar 2019.

Tsohon aikin, wanda aka kashe masa Naira biliyan 5.6, ya daina aiki ne tun a shekarar 2021, lamarin da ya jefa jami’ar cikin duhu da kuma dogaro da injinan dizal masu cin kudi.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Jami’ar BUK, Farfesa Haruna Musa, ya dora alhakin lalacewar tsohon aikin a kan rashin saka kwararrun injiniyoyin jami’ar yayin gudanar da shi. Sai dai ya ba da tabbacin cewa a wannan karon za su sanya ido sosai.

“Za mu tabbatar mun kula da wannan aiki yadda ya kamata. Inda aka zaba don kafa wannan tasha wuri ne da muke fuskantar kalubalen tsaro, don haka zai taimaka mana kwarai,” in ji Farfesa Musa.

Dokta Mustapha Abdullahi ya bayyana cewa wannan megawat daya da aka fara da shi a BUK matakin gwaji ne (pilot phase), inda akwai shirin kara karfin wutar zuwa megawat 4.5 nan gaba.

Sannan ya kara da cewa wannan bangare ne na babban shirin gwamnati na raba megawat 150 na hasken rana a fadin jihohi 36 na Najeriya da kuma birnin tarayya Abuja, domin samar da wuta mai rahusa ga al’umma.

Sama da 40,000 ne za su amfana da wannan haske wanda zai Saukaka binciken kimiyya da kyautata rayuwar dalibai a ajujuwa da dakunan kwanansu.

Afrika, Kimiya, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau Ya Koma Jam’iyyar APC
Next Post: Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere

Karin Labarai Masu Alaka

Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa Afrika
Kotu A Abuja Tabawa Goodluck Jonathan Daman Tsayawa Takara Afrika
Maulidi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu Afrika
Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya Afrika
Jami’an Askarawa A Zamfara Sun Kama Na’urorin Fashewa Da Makudan Kuɗaɗe Afrika
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gombe Ta Yi Gasar Makarantun Firamare Don Bikin Cika Shekaru 100 Na Hassan Central Afrika
  • Anyi Rashin ‘Yan Jarida 6 A Jihar Gombe Sakamakon Hatsarin Mota Labarai
  • Harin Jirgi Maras Matuki Ya Hallaka Mutane A Sudan Labarai
  • Tinubu Ya Buɗe Katafaren Kamfanin Sarrafa Lithium Domin Bunƙasa Tattalin Arziki Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Asabar 11.15.2025 Rediyo
  • An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe Afrika
  • Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
  • An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.