Gwamnatin jihar Plateau ta umarci rufe dukkan makarantun firamare da sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar, daga ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, a matsayin matakin kariya daga yaɗuwar cutar Diphtheria.
Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon samun wasu da ake zargin sun kamu da cutar a wasu ƙananan hukumomi, ciki har da Jos North, Wase, Jos South da Bassa.
A cewar gwamnatin, makarantun da suka riga suka fara karatu su ma za su rufe daga ranar Litinin, kuma za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an ba da wata sabuwar sanarwa.
Gwamnatin ta buƙaci masu makarantu, malamai, iyaye da masu kula da ɗalibai da su tabbatar da bin umarnin, tare da kiyaye yara da ɗalibai a gidajensu a lokacin da ake ci gaba da ɗaukar matakan dakile cutar.
Ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin kare lafiyar ɗalibai da ƴan makaranta, da ma’aikatan makarantu, tare da hana yiwuwar yaɗuwar cutar a tsakanin al’umma.
Gwamnatin jihar Plateau ta nemi haɗin kan jama’a da sauran masu ruwa da tsaki, tana mai cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da lafiyar al’ummar jihar.
Ta ƙara da cewa za a sanar da lokacin da za a koma makarantu da zarar an samu sauƙin halin da ake ciki.


