Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Majalisun Najeriya Sun Amince Ta Karin Kasafin Kudi
Published: March 31, 2026 at 9:11 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar talata, majalisun dokokin Najeriya suka amince da kari akan Kasafin kudin kasar zuwa Naira trillion 68 da milyan milya dari uku, wato dala bilyan 49 da milyan dubu 400, bayan da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bukaci wakilan su amince da canjin domin karfafa shirin da aka gabatar musu tun da farko cikin watan Disamba.

Shugaba Tinubu wanda yake cikin shekara ta uku da hawa kan karagar mulki, ya bullo da shirye shirye na yin garambawul ga tattalin arzikin kasar, da suka hada da janye tallafin mai dana makamashi masu tsada, da karya darajar kudin kasar, hade garambawul ga hanyoyin tara kudin haraji da zummar karfafa Kudaden shiga ga gwamnati.

A ranar 19 ga watan disemba ne shugaba Tinubu ya gabatarwa majalisa kasafin kudi na Naira trillion 58. 47, yana mai cewa zummar itace kara karfafa ci gaban tattalin arziki.

Ahalinda ake ciki kuma, wasu majiyoyi sun fadawa kamfanin dillanciin labarai na Reuters cewa, kamfanin mai na Najeriya NNPC ya kara mai da yake baiwa matatar mai ta Dangote zuwa jirage bakwai daga 5 da ya saba baiwa kamfanin cikin watannnin baya, sakamakon tashin farashin mai da yakin gabas ta tsakiya ya haddasa.

Afrika, Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Isra’ila Zata Rusa Gidajen Da Suke Iyakarta Da Lebanon
Next Post: Ministan Sufurin Najeriya Ya Ajiye Mukaminsa Domin Takarar Gwamna

Karin Labarai Masu Alaka

Zabebben Shugaban Hungary Yace Zaidawo Da Tsarin Dimokraɗiyya Afrika
An Yiwa Dokokin Kare Hakkin Yara Rikon Sakainar Kashi Labarai
An Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman Don Neman Zaman Lafiya Labarai
Ukraine Ta Aika Tawagar Kwararru Gabas Ta Tsakiya Afrika
An Gano Gawar Dan Yawon Bude Ido A Kasar Chadi Afrika
Shugaba Tinubu Ya Yayi Magana Game Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
  • Shugaba Trump Ya Jinjinawa Tinubu Kan Yaƙi Da Ta’addanci A Najeriya Afrika
  • Shugaba Donald Trump Yabada Umarnin Hana Jiragen Dakon Mai Shiga Venezuela Amurka
  • NAHCON Ta Yaba da Nasarar Hajjin 2026, Ta Fara Shirin Hajjin Shekara Mai Zuwa Amurka
  • Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Ya Bar PDP Ya Koma APC Labarai
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.