Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika
  • Yara Miliyan 16 Sun Amfana Da Azithromycin A Karkashin Shirin SARMAAN Afrika

Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
Published: September 10, 2026 at 10:48 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed Kauran Daular Usmaniyya, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Malam Abdullahi Sule, wanda aka fi sani da “Madaki”, ma’aikacin ɗaukar hoto na ENG da ke aiki da tawagar manema labarai ta Gidan Gwamnatin jihar Bauchi.

Malam Abdullahi Sule ya rasu ne a safiyar Alhamis, 10 ga Satumba, 2026, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

A cikin wata sanarwa, Gwamna Bala Mohammed ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ‘yan tawagar manema labarai ta Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi, ƙungiyar ’yan jaridu ta Najeriya, NUJ, abokai da abokan aikinsa, tare da al’ummar Jihar Bauchi baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ma’aikacin kafafen yaɗa labarai, mai ƙwazo, jajircewa, sauƙin kai da son zaman lafiya, wanda kyawawan halayensa suka sanya mutane da dama suka ƙaunace shi.

Ya ce Malam Abdullahi Sule ya kasance ma’aikaci mai biyayya da kishin aiki, wanda ya gudanar da ayyukansa cikin ƙwarewa da sadaukarwa, musamman wajen ɗaukar hotuna da adana tare da yaɗa ayyukan gwamnatin Jihar Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya ce rasuwar “Madaki” babban rashi ne ba ga iyalansa da abokan aikinsa kaɗai ba, har ma ga al’ummar kafafen yaɗa labarai da Jihar Bauchi baki ɗaya.

Ya bayyana shi a matsayin mutum mai sauƙin kai, nagarta da kyakkyawar mu’amala da jama’a, tare da nuna halin zaman lafiya a tsawon rayuwarsa.

Gwamnan ya roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya jiƙansa, Ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa, abokan aikinsa, abokansa da sauran waɗanda rasuwar ta shafa ƙarfin zuciya da haƙurin jure wannan babban rashi.

Haka kuma, Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga al’ummar kafafen yaɗa labarai da sauran masu zaman makoki da su yi haƙuri tare da tuna cewa mutuwa hanya ce da babu makawa kowane ɗan Adam zai bi.

Kuma tuni an gudanar da sallar jana’izar marigayi Malam Abdullahi Sule “Madaki” a ranar Alhamis, 10 ga Satumba, 2026, da ƙarfe 9:00 na safe, a Filin Barewa, daura da Maman Kapaya, Unguwan Kur, Railway, Bauchi.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko
Next Post: CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027

Karin Labarai Masu Alaka

APC Ta Sauya Jerin ‘Yan Takararta Bayan Nazarin Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Fidda Gwani Afrika
Pads To Prosperity: NEDC Ta Horar Da Mata 280 Kan Kera Pads A Gombe Afrika
Wani Alkali A Kotun Amurka Ya Dakatar Da Kudurin Shugaba Trump Afrika
Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Tallafa Wa ’Yan Sanda Da Motoci Afrika
Emmanuel Macron: Yakamata Wani Sashi Ya Rika Takawa Wani Sashi Birki A Tsarin Demokradiya Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Tsagaita Sakamakon Rokon Da Amurka Tayi Amurka
  • An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan Afrika
  • Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya
  • An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci Wasanni
  • Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
  • Damara Ya Tallafa Wa Gasar Karatun Al-Qur’ani Da Naira Miliyan Biyar A Bambam Afrika
  • Kungiyar Enyimba: Bamu Da Niyyar Rage Albashin ‘Yan-Wasa Wasanni
  • Kasar Ukraine Ta Yabawa Tarayyar Turai Bisa Bata Tallafi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.