Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7 Afrika
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK Afrika
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe Labarai
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya Afrika
  • ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Wayoyin Wutar Lantarki Afrika

Sabbin Shugabannin NUJ Bauchi Sun Sha Alwashin Inganta Aikin Jarida
Published: September 19, 2026 at 4:46 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Bauchi, ta gudanar da zaɓen sabbin shugabanninta, inda aka zaɓi Malam Isa Garba Gadau na Bauchi State Television (BATV) a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

Zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, ya samu halartar ’yan jarida masu kaɗa ƙuri’a 141.

Isa Garba Gadau ya kayar da Ahmed Mohammed na jaridar Peoples Daily a zaɓen kujerar shugaban ƙungiyar.

Haka kuma, Isyaku Ismail Wunti na Globe FM ya samu nasara kan Mu’azu Hassan na NTA Bauchi, inda aka zaɓe shi a matsayin ɗaya daga cikin sabbin shugabannin ƙungiyar.

Sauran waɗanda aka zaɓa ba tare da hamayya ba sun haɗa da Aliyu Sambo na BATV, wanda ya zama Mataimakin Sakatare; Khalid Idris Doya na Leadership, wanda aka zaɓa a matsayin Sakataren Kuɗi; da Abubakar Tofa na Globe FM, wanda ya zama Mai Binciken Kuɗi (Auditor).

Hajiya Adama Adamu ta Information ta zama Ma’ajin ƙungiyar, yayin da Malam Danjuma Sarki Saleh na BRC Bauchi ya zama sabon Mataimakin Shugaban NUJ reshen Jihar Bauchi.

Mataimakin Shugaban NUJ na Shiyyar Arewa maso Gabas, Mr Zare Baba, ya wakilci Shugaban NUJ na Ƙasa, Alhaji Alhassan Yahaya, wajen sanya ido kan zaɓen a madadin ƙungiyar ta ƙasa. Ya samu rakiyar Mataimakin Sakataren NUJ na Shiyyar Arewa maso Gabas, Malam Abubakar Musa Waziri.

A yayin rantsar da sabbin shugabannin, Shugaban Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Comrade Dauda M. Shayibu, ne ya jagoranci tawagar da ta gudanar da bikin rantsarwar.

Da yake jawabi, Mr Zare Baba ya yaba wa ’yan jaridar Jihar Bauchi bisa haɗin kan da suka nuna, wanda ya taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin lumana da fahimtar juna.

Ya kuma buƙaci sabbin shugabannin da sauran ’yan jarida da su ci gaba da ba da gudunmawa wajen bunƙasa aikin jarida a jihar, tare da yin aiki tare da gwamnatin Jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed, musamman wajen ci gaban kafafen yaɗa labarai na jihar.

Ya ambaci Bauchi Radio Corporation (BRC), Bauchi State Television (BATV) da sauran kafafen yaɗa labarai na al’umma da ke aiki a ƙananan hukumomi 20 na jihar.

A nasa jawabin, sabon shugaban NUJ na Jihar Bauchi, Malam Isa Garba Gadau, ya gode wa ’yan jarida bisa amincewar da suka nuna masa da kuma goyon bayan da suka ba shi.

Ya buƙaci ’yan ƙungiyar da su ci gaba da ba shi shawarwari, haɗin kai da addu’o’i domin ya samu damar sauke nauyin jagorancin da aka ɗora masa na tsawon shekaru uku.

Shi ma tsohon shugaban NUJ na Jihar Bauchi, Malam Umar Saidu, ya gode wa ’yan jarida bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake jagorantar ƙungiyar na tsawon shekaru shida.

Malam Umar Saidu ya buƙaci ’yan jarida da su bai wa sabbin shugabannin cikakken haɗin kai da goyon baya, domin su samu damar sauke nauyin da aka ɗora musu cikin nasara.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: INEC Ta Ce Zaɓen Gombe, Kwami Da Funakaye Yana Gudana Cikin Lumana
Next Post: Ƙungiyoyin Fararen Hula Sun Ƙarfafa Yaƙi Da Gurɓacewar Muhalli A Kaduna

Karin Labarai Masu Alaka

“Yan Wasan Super Eagles Sun Karbi Alkawarin Da Gwamnati Tayi Musu AFCON 2023 Labarai
Majalisar Dokokin Rivers Zata Tsige Fubara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jami’in Diflomasiyyar Da Ake Zargi Da Kisan Prime minister Ya Daukaka Kara Afrika
Ƙungiyoyin Fararen Hula Sun Ƙarfafa Yaƙi Da Gurɓacewar Muhalli A Kaduna Kimiya
Rikici Tsakanin NNPC Da Kungiyar Gwamnoni Akan Gibin Kudade Labarai
Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Kuɓutar da Yaro Daga Hannun Masu Garkuwa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Tinubu Zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 7.7
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK
  • KADCCAM Ta Yi Gargadi Kan Illolin Kona Daji Da Gurɓata Muhalli
  • Jam’iyyar PDP Ta Sallami Manyan ’Ya’yanta Biyu A Gombe
  • NUJ Ta Yi Gargadi Kan Barazana Ga ‘Yancin Aikin Jarida A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Sandan Birnin New York Sun Karyata Zargin Jefa Bom Ga Masu Zanga Zanga Amurka
  • Kasar Morocco Ta Kwashe ‘Yan Kasar Daga Sassan Ambaliyar Ruwa Afrika
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
  • PDP Ta Koka Kan Rushe-rushe, Korar Gombawa Motors da Zaɓen Kananan Hukumomi A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Tinubu Ta Ƙaddamar Da Tsarin Bada Kudi Na SPARK Afrika
  • Kadan Daga Cikin Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A Nan Amurka Amurka
  • Kwamitin Ardo Chindo Ya Buƙaci A Hana Mamaye Filayen Kiwo da Gandun Daji Afrika
  • Shugaba Tinubu Ya Isa Legas Domin Hutun Karshen Shekara Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.