Daga Mahaman Awal Garba a Kamaru
An samu tashin hankali da sassafe a ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026, a unguwar Mbanya da ke gundumar Douala ta 5 a Kamaru, sakamakon rikicin da ya kunno kai kan wanda zai gaji sarautar Akwa.
Rahotanni sun ce ƙungiyoyi biyu ne ke takaddama kan shugabancin masarautar, yayin da wasu daga cikin mazauna yankin suka nuna adawa da shirye-shiryen gudanar da bikin naɗin Sarki Din Dika, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 10 ga Oktoba mai zuwa.
A gefe guda akwai magoya bayan Louis Din Dika Akwa III, wanda a halin yanzu ke riƙe da sarautar.
A daya ɓangaren kuma, wasu mutane sun bayyana goyon bayansu ga Jean Pascal Ngando Ebongue, wanda suke cewa shi ne magajin da ya cancanta ya gaji marigayi Sarki Charles David Din Dika, wanda ya rasu a shekarar 2020.
Lamarin ya ƙara tsananta ne yayin da ɓangarorin biyu suka fafata, lamarin da ya tilasta jami’an tsaro shiga tsakani tare da amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa taron.
Rahotanni sun ce har yanzu ana ci gaba da sanya ido kan lamarin domin hana sake barkewar tashin hankali a yankin.

