Gwamnan jihar Gombe a Arewa Maso Gabashin Najeriya Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da biyan naira biliyan 10.32 a matsayin kuɗaɗen fansho ga ’yan fansho 6,665 na gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi.
Sabon biyan ya sa jimillar kuɗaɗen fanshon da gwamnatin Inuwa Yahaya ta biya tun bayan hawanta mulki a shekarar 2019 ta kai naira biliyan 44.134.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da biyan kuɗin a Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatin sa ta tarar da bashin kuɗaɗen fansho da ya haura naira biliyan 21 lokacin da ta karɓi mulki a shekarar 2019.
Ya ce bashin ya shafi kuɗaɗen fanshon ma’aikatan ƙananan hukumomi daga shekarar 2012 zuwa 2019, da kuma na ma’aikatan gwamnatin jiha daga 2014 zuwa 2019.
Gwamnan ya ce duk da ƙalubalen tattalin arziki da gwamnatin ta fuskanta, ciki har da annobar COVID-19, koma bayan tattalin arziki guda biyu, yaƙin Rasha da Ukraine, cire tallafin man fetur da kuma sauya tsarin canjin kuɗin Naira, gwamnatin ta ci gaba da ƙoƙarin biyan bashin.
A cewarsa, kafin wannan sabon biyan, gwamnatin ta riga ta biya naira biliyan 33.283 a matsayin kuɗaɗen fansho.
Ya bayyana cewa daga cikin naira biliyan 10.32 da aka amince a biya a wannan karon, naira biliyan 6.24 an ware su ne ga ’yan fansho 2,354 na gwamnatin jiha, yayin da naira biliyan 4.08 za su tafi ga ’yan fansho 4,311 na ƙananan hukumomi.
Gwamnan ya ce biyan ya shafi basussukan da suka taso a shekaru daban-daban a ƙananan hukumomin Akko, Balanga, Billiri, Dukku, Funakaye, Kwami, Nafada, Gombe, Kaltungo, Shongom da Yamaltu-Deba.
Ya kuma bayyana cewa an biya naira miliyan 299 ga tsofaffin ma’aikatan Kamfanin Gombe Investment and Property Development Company, bayan rushe kamfanin da kafa Gombe State Investment Promotion Agency.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce sabon biyan ya kammala dukkan basussukan kuɗaɗen fansho na gwamnatin jiha har zuwa Disamba 2025, yayin da kuɗaɗen fanshon da suka taso daga Janairu 2026 za a biya su a farkon shekarar 2027.
Ya ce: “Zan bar mulki ba tare da wani bashin kuɗaɗen fansho ba, Insha Allah.”
Gwamnan ya kuma ce gwamnatin na duba hanyoyin samar da tsarin da zai tabbatar da biyan kuɗaɗen fansho a nan gaba cikin sauƙi, ciki har da yiwuwar kafa tsarin fansho na gudummawa ko cire kuɗaɗen kai tsaye daga Asusun Haɗaɗɗen Kuɗaɗen Shiga na jihar.
Baya ga biyan kuɗaɗen fansho, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatin ta ɗauki matakai da dama domin inganta jin daɗin ma’aikata, ciki har da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, CONMESS da CONHESS, da kuma biyan albashi da fansho a kan lokaci.
Ya ce gwamnatin ta kuma gina wasu muhimman gine-ginen ma’aikata, ciki har da sabon sakatariyar gwamnatin jiha da Three Arms Zone, tare da gina sakatarorin ƙananan hukumomin ci gaba guda 13 da gyaran tsoffin sakatarorin ƙananan hukumomi 11.
Gwamnan ya kuma bayyana shirin gwamnatin na cika alkawarin gina katafaren sakatariya ga ƙungiyar ma’aikata ta Najeriya, NLC, reshen Jihar Gombe.
Dangane da sauye-sauyen ma’aikatan gwamnati, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce an kafa Bureau of Public Service Reforms, BPSR, domin inganta ƙwarewa, aiki da kuma samar da ingantaccen tsarin gudanar da ayyukan gwamnati.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta ɗauki malamai 1,000 da ma’aikatan lafiya sama da 440, baya ga wasu ma’aikata da aka ɗauka a ma’aikatu da hukumomin gwamnati daban-daban.
Tun da farko, Kwamishinan Kuɗi na jihar, Muhammadu Gambo Magaji, ya ce matakin biyan bashin kuɗaɗen fanshon na daga cikin manufofin gwamnatin jihar na tabbatar da kyakkyawan tsarin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da kuma riƙon amana.
A nasa jawabin, Shugaban NLC na Jihar Gombe, Aish Bello, ya yaba da matakan gwamnatin wajen kula da jin daɗin ma’aikata.
Shi ma Shugaban Ƙungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya, reshen Jihar Gombe, Muhammad Hassan Kwami, ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa ci gaba da biyan kuɗaɗen da ake bin ’yan fansho.
A madadin waɗanda suka amfana, Abdulkadir Adamu Kawu da Zainab Ishiyaku Adamu, sun gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da gwamnatin jihar bisa biyan kuɗaɗen da suka daɗe suna jira.
An gudanar da bikin ƙaddamar da biyan kuɗin tare da miƙa cak ga wasu daga cikin ’yan fansho na gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi.


