Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja Afrika
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe Afrika
  • Billiri/Balanga: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sabon Zabe, Amma Gwamnati Ta Yi Shiru – AB Ibrahim Afrika
  • Hukumomin Kashe Gobara A Gombe Sun Ƙarfafa Haɗin Kai Don Hana Gobara A Lokacin Bazara Labarai

Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa, Ya Nemi Haɗin Kai
Published: October 15, 2026 at 5:51 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa na jam’iyyar APC gabanin babban zaben 2027, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyar da mambobin kwamitin su hada kai, su kasance masu jajircewa da kuma mayar da hankali wajen ganin an sake zaben sa karo na biyu. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da kwamitin a Cibiyar Taro ta Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda ya ce APC a shirye take ta sabunta alkawarinta da ‘yan Najeriya.

Shugaban ya ce nasarar zaben da ya gabata ba za ta wadatar ba har sai jam’iyyar ta sake samun nasara a zaben 2027, yana mai cewa dole ne shugabanni da masu ruwa da tsaki su tabbatar da samun kuri’u a mazabu, kananan hukumomi da jihohinsu.

Ya kuma jaddada cewa, duk da yadda kwamitin zai kara kaimi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya, gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan mulki da kuma aiwatar da manufofin ajandar Renewed Hope.

 

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yaba da jajircewar Tinubu wajen zurfafa dimokuradiyya, yayin da ya soki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan kalaman da ya ce suna rage martabar ofishin shugaban kasa. Shettima ya kuma soki dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, bisa zargin amfani da alkaluma marasa inganci da kuma kwatanta Najeriya da wasu kasashe ba tare da la’akari da bambancin yanayinsu ba.

A nasa bangaren, shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce kwamitin zai gudanar da yakin neman zabe daga mazabu zuwa jihohi, tare da bayyana nasarorin gwamnati da manufofinta ga jama’a.

 

Gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ya ce manufofin gwamnatin Tinubu za su taimaka wajen saukaka aikin yakin neman zaben, yana mai yabawa shugaban kan cire tallafin man fetur da sauye-sauyen tsarin musayar kudaden waje da haraji.

Ya ce wadannan matakai sun taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Najeriya zuwa kashi 4.43 cikin 100, daga kashi 4.23 cikin 100 a shekarar da ta gabata, duk da cewa sun jawo wasu matsaloli ga jama’a. Uzodimma ya ce yakin neman zaben zai mayar da hankali kan manufofi da nasarorin da aka samu.

Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, Gwamnan Anambra, Charles Soludo, da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun bayyana goyon bayansu ga sake zaben Tinubu a 2027. Wike, wanda ya fito daga PDP, ya ce yana goyon bayan shugaban ne saboda jajircewarsa wajen fuskantar matsalolin da gwamnatocin baya suka kasa magancewa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da wasu manyan jiga-jigan kasa su ma sun bukaci ‘yan Najeriya su marawa Tinubu baya domin ya kammala ayyukan da ya fara.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kotu Ta Dawo Shari’ar Tsohon Minista Sirika
Next Post: NALV Da NEDC Sun Kaddamar Da Horon Makonni Biyu Ga Malaman Tsangaya Da Islamiyya

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dawo Da Dokar Zirga Zirgar Babura A Jihar Gombe Afrika
Ukraine Ta Tura Tawagar Kwarerru Zuwa Kasashen Larabawan Domin Basu Kariya Labarai
ADC Ta Kaucewa INEC Ta Gudanar Da Babban Taro Labarai
Shugaban Kasar Najeriya Ya Gabatar Da Kudi Fiye Da Naira Triliyan 58 A Matsayin Kasafin 2026 Najeriya
Gwamnan Jihar Filato Ya Karbi Katin APC Labarai
Kamfanin Mai Na NNPC Yasamu Gwaggwabar Riba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Agadez: An Gudanar Da Jana’izar Mutane Da Suka Mutu A Wani Harin Ta’addanci
  • Ilimi: Gidauniyar Danbayo Ta Tallafa Wa Ɗalibai Dubu Uku A Gombe
  • Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola A Abuja
  • Tambuwal Ya Karyata Rahotannin Shirin Komawarsa APC
  • UNICEF Ta Miƙa Kwalayen Abincin Jinya Ga Yara Masu Tamowa A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
  • Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika
  • Gaza Ga Albarusai Ga Yunwa Tsaro
  • Gwamna Namadi Ya Amince Da Naɗin Sabon Sarkin Gumel Afrika
  • Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai Sauran Duniya
  • Manchester United: Za Ta Nada Michael Carrick A Matsayin Kocin Riƙon ƙwarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.