Gwamnatin jihar Yobe ta amince da sabon tsarin albashi ga manyan ma’aikatan gwamnati, ciki har da Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Jiha, Sakatarorin Dindindin, da Manyan Akantoci da Masu Binciken Kuɗi na Jiha da ƙananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Alhassan Sule Mamudo, ya fitar, ya bayyana cewa Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Jihar, Abdullahi Musa Shehu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa, bisa sabon tsarin albashin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na Jiha zai riƙa karɓar naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu da talatin da ɗari takwas da talatin da ɗigo saba’in da biyar (₦1,430,830.75) a duk wata, yayin da kowane Sakataren Dindindin zai riƙa karɓar naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da uku da ɗari takwas da hamsin da ɗaya da ɗigo hamsin da biyar (₦1,203,851.55).
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa Babban Mai Binciken Kuɗi na Jiha da Babban Akanta na Jiha za su riƙa karɓar naira miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya da goma sha huɗu da ɗari shida da sittin da shida da ɗigo talatin da shida (₦1,114,666.36) kowannensu a kowane wata.
Abdullahi Musa Shehu ya nuna godiyarsa ga Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, bisa amincewa da sabon tsarin albashin, yana mai cewa hakan na nuna ƙudirin gwamnatin wajen inganta walwala da jin daɗin ma’aikatan gwamnati.
Ya kuma buƙaci waɗanda sabon tsarin ya shafa da sauran ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar da su rama wannan kyakkyawar niyya ta hanyar ƙara himma, jajircewa da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu, tare da inganta ayyukan da suke yi wa al’umma.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta bullo da tsare-tsare daban-daban na inganta walwala da jin daɗin ma’aikata, yayin da ake shirin aiwatar da wasu sabbin shirye-shirye domin ƙara inganta rayuwarsu da ƙarfafa ayyukan gwamnati.


