Gwamnatin jihar Gombe ta sayi kwalaye 11,518 na abinci na musamman da ake amfani da shi wajen jinyar yara masu fama da matsananciyar tamowa, wanda ya ƙunshi fiye da ledoji miliyan 1.72.
Abincin mai suna Ready-to-Use Therapeutic Food (RUTF) an tanade shi ne domin jinyar yara 11,518 da ke fama da matsananciyar tamowa a jihar.
Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ne ya miƙa abincin ga gwamnatin jihar a wani biki da aka gudanar a Otal ɗin Flourish da ke Gombe.
An sayi abincin ne ta hanyar shirin Child Nutrition Fund (CNF), wanda ke bai wa gwamnatoci damar haɗa kuɗaɗen tallafinsu da na abokan hulɗa domin ƙarfafa shirye-shiryen inganta abinci mai gina jiki.
Da take jawabi a wajen taron, shugabar ofishin UNICEF na shiyyar Bauchi, Dakta Nuzhat Rafique, ta yaba wa gwamnatin Jihar Gombe bisa ci gaba da zuba jari a fannin inganta abinci mai gina jiki ga yara.
Ta bayyana cewa za a yi amfani da abincin wajen kula da yaran da shekarunsu suka kama daga watanni shida zuwa 23, waɗanda ke fama da matsananciyar tamowa.


