Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Shari’ar Sirika: Odofin Ya Sha Tambayar Kwakwa Afrika
  • Ana Tsanmmanin Tinubu Ya Shiga Ka’aba Don Ganawa Da Allah Afrika
  • Amupitan Ya Gargadi Jami’an INEC Kan Cin Hanci Afrika
  • Keke NAPEP Ta Kashe Yara Biyar, Wasu Uku Rai Kwakwai Afrika
  • Ƙungiyar Ansaru Ta Dauki Alhakin Kashe Masussuka Afrika

Kwamitin Tsaftar Muhalli A Gombe Zai Dauki Mataki Kan Masu Babura Da Keke Napep
Published: October 31, 2026 at 1:29 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Gandun Dazuka ta jihar Gombe, Yusuf L. Jalingo, ya buƙaci al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da cikakken goyon baya da haɗin kai domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin tsaftar muhalli na wata-wata.

Kwamishinan ya yi wannan kira ne jim kaɗan bayan kammala aikin tsaftar muhalli na watan Oktoba, wanda aka gudanar a ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026.

Yusuf Jalingo ya bayyana cewa matakin bin dokokin tsaftar muhalli a wannan karon abin a yaba ne, inda ya jinjinawa al’ummar da suka fito domin share muhalli da tsaftace muhallansu.

Sai dai ya ce an samu wasu mutane da ba su bi ƙa’ida ba, waɗanda aka umarce su da su share muhallansu nan take, yayin da aka rufe wasu shaguna saboda rashin bin dokokin tsaftar muhalli.

Ya ce ma’aikatar za ta ɗauki matakan da suka dace domin dakile wannan dabi’a a yayin gudanar da tsaftar muhalli na gaba.

Ya ƙara da cewa kotun tafi-da-gidanka tana nan daram domin gurfanar da duk wani direban abin hawa da aka kama yana karya dokokin tsaftar muhalli a wuraren binciken da aka tanada.

Kwamishinan ya kuma yaba wa jami’an tsaro bisa gudummawa da ƙoƙarin da suke bayarwa wajen tabbatar da bin dokokin, tare da tabbatar da cewa za a ƙara tura jami’an tsaro zuwa wuraren da ake fama da ƙarancin jami’an ’yan sanda domin tabbatar da cikakken bin ƙa’ida.

Wakilinmu, wanda ya sa ido kan yadda aikin ya gudana tare da kwamitin tsaftar muhalli, ya rawaito cewa manyan wuraren kasuwanci da suka haɗa da babbar kasuwar Gombe da Dankombo Mega Park sun kasance a rufe, lamarin da ke nuna bin dokokin tsaftar muhalli.

Sai dai an ga wasu manyan motocin dakon kaya suna zirga-zirga a yankunan Liji da New Mile Three a lokacin gudanar da aikin.

Labarai

Post navigation

Previous Post: INEC Ta Amince Da Pantami Da Gwarzo Su Ci Gaba Da Takarar Gwamna

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Ruwa Ta Gombe Ta Horas Da Ma’aikatan Sashen Kasuwanci Kan Ka’idojin Aiki Afrika
Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
Kuɗaɗen Da EFCC Ta Kwato Za Su Tallafa Wa Shirin Lamunin Karatu Afrika
Shugaban Amurka Donald Trump Yace Bai Taba Shiga Jirgin Jeffrey Epstein Ba Labarai
Dakaru Sun Hallaka ’Yan Ta’adda Masu Yawa – DHQ Afrika
Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Kwamitin Tsaftar Muhalli A Gombe Zai Dauki Mataki Kan Masu Babura Da Keke Napep
  • INEC Ta Amince Da Pantami Da Gwarzo Su Ci Gaba Da Takarar Gwamna
  • Ahmed Gara Ya Dakatar Da Ayyukan Tallafa Wa Al’umma A Gombe
  • Shari’ar Sirika: Odofin Ya Sha Tambayar Kwakwa
  • Ana Tsanmmanin Tinubu Ya Shiga Ka’aba Don Ganawa Da Allah

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Isra’ila Zata Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
  • Jamhuriyar Nijar Ta Fitar Da Doka Domin Kare ‘Yancin ‘Yan Kasar Tsaro
  • Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Kungiyar Kwadago Ta Shirya Zanga-Zanga A Najeriya Najeriya
  • Matar El-Rufai Ta Roƙi Tinubu Ya Tabbatar An Yi Wa Mijinta Adalci Afrika
  • Muhawara Mai Zafi Tsakanin APC da ADC Shirye-Shirye
  • Shugaba Tinubu Yasa Hannu Kan Dokar Kasafin 2026 Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.