Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Tinubu Ya Maye Gurbin Badaru Da Tsohon Soja
Published: December 2, 2025 at 9:56 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya zabi wani tsohon babban Hafsan Sojoji ya maye gurbin ministan tsaron Kasar wanda yayi murbus jiya Litinin, a lokacin da akasami karin sace sacen mutane, da hare haren ‘yan ta’addar dake ikirarin Musulunci a Arewacin Kasar, lamari da ya kai ga shugaban kasar ayyana dokar tabaci.

Dan shekaru 58 da haifuwa, Janar Christopher Musa, ya rike mukamin babban Hafsan mayakan Najeriya daga 2023 zuwa watan oktobann bana. Zai maye gurbin Mal Badaru Abubakar tsohon gwamna daga Arewacin Najeriya, wanda yayi murabus, bisa dalilan rashin koshin lafiya.

Shugaba Tinubu ya bada sanarwar nadin ne, a cikin wasika da ya aike wa majalisa, kamar yadda ofishinnsa  ya fada.

Wannan nadin yana zuwa ne ‘yan kwanaki kacal, bayan da shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci,  a zaman martani ga karin tashe tashen hankula a kasar.

Har yanzu ba’a gano dalibai su sama da maitan da ‘yan bindiga suka sace a wata makarantar darikar Katolika ranar 24 ga watan nuwamban nan data kare. Suna daga cikin akalla mutane 402 da aka sace a kasar daga tsakiyar watan Nuwamba, kamar yadda MDD ta bayyana.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Janar Christopher Zai Maye Gurbin Ministan Tsaron Najeriya
Next Post: Kocin Ranchers Bees Ya Yi Murabus

Karin Labarai Masu Alaka

Zargin Fitar Da Bayanan Masu Zabe A Najeriya Afrika
Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika
Kotu Ta Bada Belin Abubakar Malami Bisa Wasu Sharruda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Baba Malam Ya Lallasa Abokan Hamayya Da Kuri’u Sama Da Dubu 236 A Zaben Fidda Gwani Afrika
NITDA Da GOSIDEC Sun Horar Da Ma’aikatan Gombe Don Inganta Ayyukan Gwamnati Afrika
Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Farashin Mai A Kasuwannin Duniya Yayi ƙasa Kadan Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama Labarai
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • An Samu Bullar Cutar COVID 19 A Najeriya Afrika
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji A Kauyen Wanka Jihar Filato Afrika
  • Rundunar Tsaro Suna Cigaba Da Nasara Akan ‘Yan Ta’adda Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.