AFCON ChelIe Ya Fidda Sunayen ‘Yan Wasan Super Eagles Na Karshe mutum 28 Don Gasar AFCON Ta Morocco 2025
Babban kocin Najeriya, Eric Sékou Chelle, ya bayyana ‘yan wasa 28 da za su fafata a gasar cin kofin Afirka karo na 35, Super Eagles ta zama zakarun Afirka sau uku inda za su shirya zuwa wasa a Morocco na a cikin kwanaki 10.
Chelle ya ci gaba da nuna goyon baya ga wasu taurarin Najeriya, inda ya sanya Stanley Nwabali a matsayin mai tsaron gida na farko tare da masu tsaron baya Calvin Bassey, Semi Ajayi, Zaidu Sanusi, ‘yan wasan tsakiya Wilfred Ndidi da Frank Onyeka, da kuma ‘yan wasan gaba biyu Victor Osimhen da Ademola Lookman. Su ne ke jagorantar kungiyar.
Kocin ya kuma hada da Chidozie Awaziem, Bright Osayi-Samuel, Fisayo Dele-Bashiru, Raphael Onyedika, Samuel Chukwueze, da Simon Moses.
An gayyaci Francis Uzoho, wanda yanzu haka yake zaune a Cyprus, da kuma mai tsaron baya Igoh Ogbu da kuma ɗan wasan gaba Paul Onuachu.
‘Yan wasa biyar sun sami gayyatar farko zuwa Super Eagles: ɗan wasan baya na dama na Ingila Ryan Alebiosu, ‘yan wasan tsakiya Usman Muhammed, Ebenezer Akinsanmiro, Tochukwu Nnadi, da kuma ɗan wasan gaba na Croatia Salim Fago Lawal.
An shirya Super Eagles za su buga wasan sada zumunci mai ƙarfi da Pharaohs na Masar a ranar Talata, 16 ga Disamba, a filin wasa na Cairo International Stadium.
Wasan zai bai wa Chelle damar ƙarshe ta tantance ‘yan wasansa kafin ƙungiyar ta tashi daga Cairo a cikin jirgi zuwa Fès, inda za su fafata a wasannin rukuni na C.
Najeriya za ta fara fafatawa da Taifa Stars na Tanzania a ranar 23 ga Disamba, kafin ta fafata da Tunisia a ranar 27 ga Disamba sannan ta kammala fafatawar rukuni da Uganda a ranar 30 ga Disamba.
‘Ga jerin Yan wasan Najeriya 28 da za su fafata a AFCON 2025 (Morocco)
Masu tsaron gida:
Stanley Nwabali (Chippa United, Afirka ta Kudu); Amas Obasogie (Singida Blackstars, Tanzania); Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus)
Masu tsaron gida:
Calvin Bassey (Fulham FC, Ingila); Semi Ajayi (Hull City, Ingila); Bright Osayi-Samuel (Birmingham City, Ingila); Bruno Onyemaechi (Olympiakos, Girka); Chidozie Awaziem (Nantes FC, Faransa); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Igoh Ogbu (Slavia Prague, Jamhuriyar Czech); Ryan Alebiosu (Blackburn Rovers, Ingila)
‘Yan wasan tsakiya:
Alex Iwobi (Fulham FC, Ingila); Frank Onyeka (Brentford FC, Ingila); Wilfred Ndidi (Besiktas FC, Turkiyya); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Tochukwu Nnadi (Zulte Waregem, Belgium); Fisayo Dele-Bashiru (SS Lazio, Italiya); Ebenezer Akinsanmiro (Pisa SC, Italiya); Usman Muhammed (Ironi Tiberias, Isra’ila)
‘Yan wasan gaba:
Ademola Lookman (Atalanta BC, Italiya); Samuel Chukwueze (Fulham FC, Ingila); Victor Osimhen (Galatasaray FC, Turkiyya); Simon Moses (Paris FC, Faransa); Chidera Ejuke (Sevilla FC, Spain); Akor Adams (Sevilla FC, Spain); Paul Onuachu (Trabzonspor AS, Turkiyya); Cyriel Dessers (Panathinaikos FC, Girka); Salim Fago Lawal (NK Istra 1961, Croatia)
Super Eagles za ta yi kokarin lashe kambun nahiyar karo na hudu, shekaru 11 bayan nasarar da ta samu a Afirka ta Kudu.


