Rahotanni daga Afirka ta kudu suna kara bayyana yadda aka yaudari wasu ‘yan kasar suka tafi Rasha da sunan aikin tsaro ko makamancin haka, sai suka sami kansu a fagen daga a Ukraine, wani mahaifi Dubandlela yana cikin annashuwa da alfahiri lokacin da dansa dan shekaru 20 da haifuwa ya sanya hanu cikin watan Yulin bana, zai tafi Rasha inda za’a horas da jami’in tsaro da zai bada kariya ga masu hanu da shuni ko masu fada a ji.
Wata biyar bayan tafiyarsa, yanzu Dubandlela yana cike da takaici da zullumi, inda Dansa ya fada hanun mayaudara daga kungiyoyin sojojin haya, inda dansa da wasu akalla ‘yan kasar Afirka ta kudu 16 aka dauke su kuma aka tura fagen yaki a Ukraine.
Dubandlela yana aibunta kansa kan hali da dansa ya sami kansa a ciki, kuma Kakakin shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramphosa, yace gwamnati tana “daukar batun da matukar muhimmanci.”
Yace kokarin kubutar da matasan yana da sarkakiya sosai, Kuma suna magana da dukkan sassan a yakin tsakanin Rasha da Ukraine, amma Vincent Magwenya yace sun fi bada karfi ne a magana da Rasha saboda an tura matasan ne ba shiri cikin rundunar mayakanta, Ya kara da cewa sun sami labari cewa matasan suna cikin hadari sosai a yankin Donbas.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fada, yaudarar da aka yi wa matasan ba zata rasa nasaba da zargin da aka yi wa ‘yar tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, Lamari da ya tilasta mata yin murabus daga mjalaisar dokokin kasar.
Ma’aikatar harkokin wajen Rashar bata maida martani ba, da aka nemi jin ta bakinta a rubuce kan hanyoyin yaudarar matasan, da halinda suke ciki a halin yanzu


