Shugaba Faustin Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, zai nemi komawa kan kujerarsa a wa’adi na uku a zaben da za a gudanar ranar lahadi a kasar, bayan da ya shafe shekaru 10 a kan wannan kujera.
Touadera mai shekaru 68 da haihuwa, yana amfani da irin dabarun da aka gani daga wasu kasashen Afirka domin kara wa’adinsa a kan mulki, a bayan da ya jagoranci gudanar da kuri’ar raba gardama domin kawar da tanadin wa’adi biyu da tsarin mulki ya tanadar.
A shekarar 2018, kasar ta zamo ta farko a yankin tsakiya da yammacin Afirka da ta gayyato rundunar sojojin haya ta Wagner ta kasar Rasha, kuma daga bisani kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun bi sahunta.
A shekarar 2022, gwamnatin Touadera ta zamo ta farko a nahiyar Afirka, kuma ta biyu a duk duniya, da ta fara amincewa da kudin Crypto na Bitcoin.
Touadera, wanda yake yakin neman zabe bisa tsaro da yace ya karfafa a kasar, ya kuma yi alkawarin samar da kayayyakin bukatu kamar hanyoyi da layukan dogo na jiragen kasa.
Masu fashin baki sun ce Touadera ake kyautata zaton zai lashe wannan zabe.


