Alh. Aliko Dangote ya jaddada wani zargi da ya shafi shugaban sashen kula da albarkatun Man Fetur na Najeriya,
Dangote, dai ya yi karin bayani da cewa Inginiya Farouk Ahmed, ya kashe dala miliyan biyu don biyawa ‘yan’yan sa kudin makarantar gaba da sakandare, inda ya kara da cewa a cikin kudin, ya kashewa dan sa
Faisal dala $210,000 don yin digiri na biyu a fannin kasuwanci a jami’ar Harvard da ke kasar Amurka.
Shugaban hadakar kamfanin Aliko Dangote, ya bayyana zargin da yake yiwa shugaban sashen kula da albarkatun man fetur na kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, inda ya ke zargin sa da kashe miliyoyin daloli don biyawa ‘ya’yan sa kudin makaranta a kasashen waje.

A ranar Lahadi, Alhaji Dangote ya zargi Farouk Ahmed da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, abin da yace yana kawo koma baya wajen ci gabankasar a fannoni da dama.
Yayin da yake magana a wani taro na karawa juna sani a matatar Man Dangote, Alhaji Aliko ya zargi shugabancin na NMDPRA da hada kai da ‘yan kasuwar waje, da masu shigo da Mai daga waje domin su kawo tazgaro ga matatar Mmai na cikin gida ta hanyar bayar da lasisin shigo da kayyakin Man Fetur.
Alhaji Dangote ya yi ikirarin cewa Farouk Ahmed yana wadaka da kudin da ya zarce albashin sa. Ya yi zargin cewa hudu daga cikin ‘ya’yan sa dake makarantar sakandare a kasar Switzerland, inda ake kashe musu miliyoyin daloli.
Ya ce wannan facaka abu ne da ya kamata a bincika don yana nuni da almundahana da kudin gwamnati na bangaren lura da harkokin Man Fetur.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Alh. Aliko Dangote, a ranar Litinin, ya kara da zargin cewa, Alhaji Ahmed ya kashewa ‘ya’yan sa fiye da dala miliyan 5 a kudin makarantar sakandare a Switzerland.
Dangote ya lissafa ‘ya’yan da makarantar su, da suka hada kamar haka;
Faisal Farouk da ya yi makarantar Montreux
Farouk Jr kwalejin Aiglon
Ashraf Farouk Institute Le Rosey
Sai kuma Farhana Farouk da ta yi makarantar La Garenne International
Ya ce ko wanne daga cikin su ya yi shekara 6 a makaranta.
A cewar sa abin da aka kiyasta na kudaden makarantar sakandire da ake biya duk shekara da kudin jirgi da kudin batarwa kowanne da ya tashi kan dala $200,000 jimillar dala $4, 800,000 na yara hudu. Kwatankwacin naira Biliyan daya da miliyan dari da ashirin kudin Najeriya.
Bugu da kari, Dangote ya ce Farouk Ahmed ya kashewa yaran sa 4 dala miliyan biyu kudin makarantar gaba da sakandare, ya kara da cewa ya kashewa dan sa Faisal dala $200,000 don karo karatu a matakin digiri na biyu a harkar kasuwanci a jami’ar Harvard.
Baki daya an kashewa yara, kama daga kudin makaranta, kudin kashewa da kudin tikitin jirgi na kaiwa da komwa, jimilla kimanin dala$125,000 a kowace shekara na yara hudu kacal, idan aka hada na shekaru shekaru hudu zai kama $500,000 a tara sau hudu zai kama $2,000,000.
Faisal wanda ya kammala karatun digiri na biyu a wannan shekarar ta 2025 a jami’ara Harward da ke nan Amurka, an biya mishi $150,000 da dala $60,000 na cin abinci, tikiti da sauran makulashe kuwa suka kama dala $210, 000 a wannan shekarar kawai ta 2025.


