Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta
Published: November 26, 2025 at 4:04 PM | By: Nafisa Ahmad

Wakilin Amurka, Massad Boulos, ya ce Amurka ta gabatarwa da sassan dake yakar juna a kasar Sudan wani shiri na kulla tsagaita wuta, amma kuma babu daya daga cikin bangarorin da ya bayyana amincewarsa da shirin ya zuwa yanzu.

Boulos yace duk da cewa babu wanda ya nuna rashin yarda da abubuwan dake kumshe a cikin shirin da Amurka ta gabatar, rundunar sojojin Sudan ta shimfida wasu ka’idojinta wadanda yace ba za a iya cimmawa ba.

Mai yakar rundunar sojoji a wannan fadan, Rundunar Dakarun wucin gadi ta RSF, ta ayyana tsagaita wuta na radin kanta jiya Litinin kamar yadda Amurka ta nema. Amma a yau Talatar nan, rundunar sojojin Sudan ta ce ta fatattaki wani harin da aka kai kan wani sansaninta dake Babanusa a Jihar Kordofan ta yamma, inda a nan yanzu bakin daga take a yakin na Sudan.

A makon da ya shige shugaba Donald Trump yace zai sa baki domin ganin an kawo karshen  wannan fadan daya barke a tsakanin rundunar soja da ta RSF a watan Afrilun 2023 a sanadin gwagwarmayar neman shugabanci tsakanin sassan biyu. Wannan rikici ya haddasa bala’in yunwa mai tsanani da kashe-kashen kabilanci da kuma raba miliyoyi da matsugunansu.

A halin da ake ciki, kungiyar agaji ta likitoci mai suna Medicine Sans Frontier, ko MSF a takaice, ta fada a yau Talata cewa ta janye ma’aikatanta daga wani asibitin dake Darfur, a bayan da aka harbe wani mai tura keken daukar marasa lafiya har lahira.

Kungiyar tayi kira ga dakarun rundunar RSF dake rike da wannan yanki da su tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatan asibitin dake yankin tsakiyar Darfur.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya
Next Post: Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Guinea Bissau

Karin Labarai Masu Alaka

Farashin Danyen Mai Ya Fadi A Kasuwar Duniya Afrika
Gwamnatin Soji A Nijar Ta Hana Fitar Da Albarkatun Kasa Afrika
Jiragen Saman Yakin Najeriya Suka Gurgunta Yunkurin Juyin Mulki A Benin Afrika
Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
Fiye Da Fararen Hula 1000 Yunwa Ta Kashe A Sudan Afrika
‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Kashe Mutum 2 Da Suka Ba ‘Yan-Matan (GGCSS Maga) Kariya! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki Labarai
  • Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
  • Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika A Wannan Makon Wasanni
  • Amurka Ta Kai ‘Yan Cirani Kamaru Afrika
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.