Amurka ta girke jirage marasa matuki, tare da sojoji 200 a Najeriya domin su horar da sojojin kasar su kuma taimaka musu da bayanan sirri, a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda a arewacin kasar, kamar yadda jami’an Amurka da Nigeria suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Jami’an sun ce sojojin na Amurka basa shiga fagen daga tare dana Nigeria, kuma jiragen drone din suna daukan bayanan sirri ne kawai, basa kai hari.
Amma duk da haka girke sojojin na Amurka, wanda ya biyo bayan harin da ta kai arewa maso yammacin kasar a kashen shekarar data gabata, na nuna Amurka na sake shiga fadan dakile ‘yan ta’adda da kungiyoyi masu alaka da al-Qa’ida a arewacin Afirka.
A da Amurka na da sansanin jiragen drone a kasar Niger da kudin sa ya kai dala miliyan 100, tare da sojoji kimanin 1000 dake sa ido a yankin na Sahel, amma an rufe Wajen a shekarar 2024 bayan da gwamnatin sojin Niger ta bukaci da su fice daga nan.


