Amurka ta kwadaitawa Ukraine cewa zata bata tsaro kwatankwacin abunda NATO ta alkawartawa membobinta, a ci gaba da shawarwari da ake yi a Jamus tsakanin wakilan Amurka da Turai da ukrine a Berlin, inda ake samun rahotannin ci gaba a zaman da wakilan suka yi ranar litinin, sai dai an kasa samun daidaito kan baiwa Rasha wani bangaren kasar Ukraine.
Wakilan Amurka a taron su suka gabatar da tayin da hukumomi a Washington suka yi na bada kariya ta musamman ga Ukraine, amma sunyi kashedin cewa wannan tayin ba zai dore ba, mudddin Ukraine bata karba a yanzu ba.
Shawarwarin da ake yi a babban birnin Jamus din, shugabannin turai sun nuna kwarin guiwar samo bakin zaren warware yaki mafi muni a turai, tun bayan kamma yakin duniya na biyu.
Har yanzu dai Moscow bata ce zata amince da sauye sauyen da aka yi wa daftarin zaman lafiya a zaman da aka yi a Berlin ba, kuma bata nuna alamar zata yi hakan ba.
“Muna kokarin ganin an cimma yarjejeniyar,” shugaba Trump ya fada a fadar white House bayanda yayi magana da jiga jigan shawarwarin da ake yi a Berlin, yayinda jami’an suke halartar wata liyafar cin abincin dare.
Wani binciken ra’ayin jama’a da aka yi, ya nuna galibin ‘yan kasar Ukraine basa goyon bayan kasar ta bawa Rasha wani bangaren kasar.


