An fara bude makarantu a fadin wasu sassan arewacin Najeriya ranar Litinin, bayan watanni da rufe makarantun, sakamakon sace daruruwan dalibai a cikin watan Nuwamban bara.
Sace sacen daliban a bara ya nuna irin matsalolin tsaro da sashen ilmi yake fuskanta a yankin da yake fama da fitinar kungiyoyi barayi da mayakan sakai dake ikirarin bin tafarkin Islama.
An bude makarantun ne, bayan da wata sanarwa da gwamantin tarayya ta fitar a cikin watan jiya ta cewa daukan wasu karin matakan tsaro ya inganta yanayi da zai kai a bude makarantun, sai dai gwamnatin tarayyar bata bada karin bayani ba kan furucin nata.
Ga Rahoton Zainab Babaji Daga Jos a Najeriya


