Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

An Gargaɗi Mazauna Maiduguri Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya
Published: March 13, 2026 at 5:12 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

An Gargaɗi Mazauna Maiduguri Su Guji Yaɗa Labaran Ƙarya

Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri

An gargaɗi mazauna birnin Maiduguri da su guji wallafawa da kuma yaɗa labaran ƙarya a kafofin sadarwar zamani domin kauce wa haifar da tashin hankali a cikin al’umma.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafofin sadarwar zamani da ke cewa an samu wani abu da ake kyautata zaton abin fashewa ne a harabar wani masallaci da ke unguwar Abuja Sheraton a Maiduguri.

Ya ce, “Wannan labari ba shi da tushe balle makama, domin babu wani abin fashewa da jami’an tsaro suka samu wanda zai zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.”

Hakazalika, ya yi gargaɗin cewa, “Yaɗa bayanai marasa tushe na iya sanya mazauna birnin Maiduguri cikin firgici tare da kawo cikas ga ƙoƙarin hukumomin tsaro na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.”

A cewarsa, “Ya kamata jama’a su riƙa tabbatar da sahihancin labarai daga amintattun majiyoyi kafin su yaɗa su a kafofin sadarwar zamani.”

Shi ma Malam Bukar Abubakar ya ce, “Akwai buƙatar jama’a su tsaftace yadda suke amfani da kafofin sadarwa domin kauce wa haddasa husuma a cikin al’umma.”

Wasu mazauna birnin, ciki har da Mathew Joshua da Ahmed Mahmud, sun ce, “Duk da matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan jihar, akwai buƙatar jama’a su kwantar da hankalinsu tare da gujewa yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da su ba, waɗanda ka iya ƙara dagula zaman lafiya a Maiduguri.”

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Trump Tana Cigaba Da Korar Baki Daga Amurka
Next Post: Yunkurin Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi Na Kara Kankama A Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Guguwa Mai Karfi Ta Raunata Dubban Mutane A Madagascar Labarai
Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
Magungunan Cutar Kolera Sun Makale A Dubai Afrika
Yunkurin Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi Na Kara Kankama A Najeriya Labarai
An Kai Hari Kan Masu Hakar Ma’adanai A Kasar Mali Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
  • ‘Yan Sandan Gombe Sun Yi Taron Gaggawa Da Jam’iyyun Siyasa Da INEC Kan Tsaro Labarai
  • ‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisar Dattawan Amurka Ta Amince Da Wata Doka Amurka
  • Harkar Zirga Zirgar Jiragen Sama Ya Bunkasa A Kenya Afrika
  • Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
  • AFCON 2025, Jerin Abubuwan Da Aka Haramta Wa Magoya Baya Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.