Hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya tace kawancen aiki data kulla da Kotun Sulhu ta jihar Kano (Kano Multi-Door Court) yana haifar da sakamako mai kyau, ta fuskar warware matsalolin danne hakkoki a tsakanin al’uma.
A taron kaddamar da sabbin mambobin majalisar kula da ayyukan Kotun, shugaban Ofishin shiyyar Kano na hukumar Abdullahi Shehu yace, aiki kafa da kafa da Kotun Sulhun ta Kano na taimakawa bangaren sasanta Jama’a da sulhunta su na hukumar, inda a cewar sa, hadin gwiwar ke bada dama su dai-daita mutanen dake takaddama da juna cikin karamin lokaci.
An kafa Kotun Sulhu ta Kano ne tun kimanin shekaru 20 da suka shude, domin sasanta mutanen dake takaddama da juna akan al’amura daban daban, a wani mataki na rage cunkoson kararraki a gaban kotuna da-ma gidajen yari.
Kotun mai hurumin hukunci dai-dai dana babbar kotun jiha (State High Court), na sauraron kararraki ko korafe-korafe da suka shafi Cinikayya, takaddamar Aure, hakkin makwaftaka da sauran batutuwan yau da kullum na rayuwar Jama’a.
Kotun na aiki tare da hukumomin tsaro, musamman hukumar ‘yan sanda da kungiyoyin kare hakkin bil’adama, Malaman addini, shugabanni al’uma da masu rike da sarautu.
Babbar Jojin Kano, mai shari’a Dije Aboki, ta bukaci Jama’a su kara kaimi wajen amfani da damammakin da Koton ke bayarwa na saukaka shari’u da kuma fito da hakki babu bata lokaci.
Cunkoson kararraki a gaban alkalai a Najeriya na cikin manyan kalubalen da ‘yan kasar ke fuskanta wajen samun adalci a kotuna, musamman wadanda ke tsare a gidajen yari na suna dakon a yanke musu hukunci.


