An kashe wasu mutane da dama a harin da aka kai da maraicen talata da jirgin saman drone a kusa da matatar mai mafi girma a kasar Sudan.
Rundunar sojojin wucin gadi ta RSF, wadda tun shekarar 2023 take gwabza yaki da rundunar sojojin kasar ta Sudan, ta ce sojojin gwamnati ne suka kai hari kan matatar dake Heglig, kwana guda a bayan da dakarun RSF suka kwace wannan matata dake kusa da bakin iyakar kasar da Sudan ta Kudu.
Dukkan sassan biyu sun fada ma kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa ba su da cikakken adadin wadanda aka kashe ko aka ji ma rauni, amma kafofin labarai a yankin sun ce an kashe shugabanni 7 na wasu kabilu tare da sojojin rundunar RSF
Rundunar RSF ta kuma ce akwai sojojin Sudan ta Kudu a wannan harin da ta ce ya saba dokoki na kasa da kasa.
Rundunar sojojin Sudan ta tabbatar da kai hari da jiragen drone wadanda ta ce an auna su ne a kan mayakan rundunar RSF.
Gwamnatin jihar Unity ta Sudan ta Kudu ta tabbatar da kashe sojoji uku na Sudan ta Kudu.


