Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

An Kama Maharan Bom Din Maiduguri
Published: January 7, 2026 at 5:48 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sojoji sun kama ƙarin mutane 8 da ake zargi da hannu a harin bam na masallacin Borno

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun kama ƙarin mutane takwas da ake zargi da hannun su a harin bam da wani mai tayar da kai ya kai a wani masallaci da ke Maiduguri, jihar Borno.

Wannan na zuwa ne kasa da kwana uku bayan sojoji sun kama wanda ake zargin shine ya shirya harin, mai suna Sheriff Umar, a babban birnin jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa harin kunar bakin wake ya faru ne a ranar 24 ga Disamba na shekarar 2025, lokacin da wani mai tayar da bam ya tarwatsa na’urar fashewa (IED) a cikin wani masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla masu ibada biyar tare da jikkata wasu 35.

A cikin wata sanarwa, jami’in hulda da jama’a na rundunar Operation hadin kai, Sani Uba, ya bayyana cewa an kama waɗannan mutanen ne a wani samame da aka gudanar a unguwar Yan Lemu da ke karamar hukumar Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa.

Ya ce, Binciken da aka yi a gidan da ake zargin ya haifar da gano maƙudan kuɗaɗe, wayoyin hannu, takardun shaidar tantancewa, katunan ATM, kayan ado da wasu kayan sirri na amfanin kai, waɗanda a halin yanzu haka ake gudanar binciken shaidu akan su.

Ya ƙara da cewa, wani da ake tsare da shi tuni ya tantance wasu daga cikin manyan masu hannu a lamarin a matsayin waɗanda suka kawo kayan da aka yi amfani da su wajen ƙera bam ɗin.

Ya ƙara da cewa, Sauran mutanen da ke zaune a gidan suma an samo alaƙarsu da wannan ƙungiya.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kotu Ta Bada Belin Abubakar Malami Bisa Wasu Sharruda
Next Post: Martanin Wasu ‘Yan Najeriya Ga Ministan Labarai Bisa Korar Dadiminsa

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya Labarai
‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana Afrika
Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya Amurka
Ministan Harkokin Wajen Iran Yagana Da Shugaban Sa’ido Akan Nukiliya Afrika
Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Ta Rufe Sararin Samaniyar Ta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika
  • Ana Cigaba Da Kai Kayan Agaji Kasar Morocco Sakamakon Tsananin Hunturu Afrika
  • Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Kasar Nijar Afrika
  • Kauran Bauchi: Muna Nan A PDP Daram! Siyasa
  • Darajar Kudin Afirka Ta Kudu Ya Tashi Afrika
  • Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani Najeriya
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Guinea-Bissau Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.