Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama wani likita da ake zargi da jigilar kayan magani daga Jihar Sokoto zuwa wasu kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke aiki a sassan jihar Kwara.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na gidan Gwamnatin Jihar Kwara a ranar Juma’a.
Rahotanni sun ce an kama likitan ne a Jebba, cikin Karamar Hukumar Moro, bayan samun bayanan sirri da suka hada shi da wata hanyar kai magunguna ga kungiyoyin ‘yan bindigar.
An ce kama ire iren sa, yana daya daga cikin matakan da ake dauka domin dakile hanyoyin da ke tallafa wa miyagun kungiyoyi a yankin.
Majiyoyin tsaro sun ce ‘yan bindigar sun kara yawan neman kulawar likita, musamman wajen magance raunukan harbin bindiga da suke samu yayin artabu da jami’an tsaro.
Wannan karuwar bukatar magunguna ta jawo hankalin hukumomin tsaro da ke sa ido kan zirga-zirgar haramtattun kayayyaki.
Wani jami’in tsaro ya yi gargadin cewa cibiyoyin lafiya da ke kusa da dazuka na iya fuskantar karin barazana, domin miyagun mutane na iya kai farmaki don neman kulawar gaggawa.


