An fara kidaya kuri’u a kasar Guinea-Conakry, bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar lahadi, zaben da ake kyautata zaton shugaban gwamnatin mulkin soja, Mamady Doumbouya, wanda ya kwace mulki a shekarar 2021, shine zai lashe cikin sauki.
Tsohon kwamandan rundunar zaratan sojojin na Guinea, ya fuskanci ‘yan takara 8 a wannan zaben na jiya, wanda in ya lashe, zai ba shi wa’adin shekaru 7 a kan karagar mulki, tare da kawo karshen shirin maido da mulkin farar hula.
Hambararren shugaban Guinea-Conakry, Alpha Conde, da dadadden madugun hamayya Cellou Dalein Diallo, har yanzu su na zaman gudun hijira a waje.
Babu wani tashin hankali da aka samu a lokacin zaben, inda a babban birnin kasar watau Conakry, wadanda suka fito ba su da yawa. Amma akasarin jama’a sun ce an riga da an san yadda zaben zai kaya, don haka ba sai sun bata lokaci wajen zuwa jefa kuri’a ba.
Doumbouya, wanda ya sanya babbar riga fara tare da matarsa, ya jefa kuri’arsa a wata mazabar dake wani asibiti a Conakry.
Ana sa ran samun sakamakon farko na zaben nan da kwana biyu ko uku.


