Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ana Cigaba Da Tattaunawa Tsakanin Trump Da Zelensky Domin Tsagaita Wuta A Ukraine
Published: December 29, 2025 at 11:01 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Donald Trump na Amurka ya fada cewa shi da shugaba Volodymyr Zekensky na Ukraine sun kara gusawa ga cimma daidaituwa a kan yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine, amma kuma yace har yanzu ba a cimma matsaya guda ba, a kan muhimmin batun nan na makomar yankin Donbas ba.

Shugabannin biyu sun yi magana a taron ‘yan jarida na hadin guiwa bayan tattaunawarsu a gidan shugaba Trump na Mar-a-Lago dake jihar Florida.

Shugabannin biyu, sun ce an samu ci gaba a kan wasu muhimman batutuwa biyu masu sarkakiya, watau tabbatar da tsaron kasar Ukraine da yadda za a raba yankin Donbas na gabashin ukraine, yankin da Rasha ke neman mallaka baki dayansa.

Trump yace nan da ‘yan makonni kadan za a san ko za a iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Zelensky yace an cimma yarjejeniya a kan batun tabbatar da tsaron kasar ukraine a nan gaba, watau ba kasar Garanti na tsaro daga duk wani harin Rasha ko wata kasa amma shugaba Trump ya nuna taka tsantsa kan wannan batu, yana mai fadin cewa an cimma kashi 95 cikin 100 ne a batun ba kasar ta ukraine garanti na tsaro.

Yace ana sa ran kasashen Turai zasu dauki alhakin wannan tare da goyon bayan Amurka.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza
Next Post: Shugaban Ƙasar Koriya Ta Arewa Ya Halarci Gwajin Makami Mai Linzamin Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Botswana Na Samun Kudaden Shiga Da Lu’ulu’u Labarai
Ukraine Takai Hari Wajen Kera Makami Mai Linzami A Rasha Labarai
Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan Labarai
Kamfanin Hakar Ma’adanai Na Kasar Kanada Ya Cigaban Da Aikinsa Labarai
An Gano Wani Kurkukun Sirri Da Ake Azaftar Da Mutane A Kasar Libya Afrika
Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
  • Shari’ar Abubakar Malami Ta Kaura Zuwa Sabon Alkali Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kwankwaso: Gwamnatin Kano Tamuce Baki Daya, Tafiya APC Allah Ya Raka Taki Gona! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Aikin Layin Dogon Kasar Uganda Zai Hade Kasar Da Tanzania Da Kwango Kimiya
  • Harin Ukraine Yayi Mummunan Barna A Rasha Afrika
  • Asusun IMF Zasu Ziyarci Kasar Gabon Afrika
  • Manya-Manyan Wasannin Wannan Makon Wasanni
  • Rasha Takai Mummunan Hari Birnin Kyiv Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.