Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Gombe ta fara duba lafiyar masu niyyar zuwa aikin Hajji na shekarar 2026 a Asibitin kwarerru na jihar Gombe.
An shirya wannan Duba lafiyar ne domin tantance halin lafiyar masu niyyar tafiya kasa mai tsarki ta Saudiyya, kafin a fara tafiya.
Da yake magana a wajen kaddamar da aikin duba lafiyar, Sakataren hukumar, Alhaji Sa’adu Hassan, ya bayyana cewa duba lafiyar wajibi ne, kuma yana daga cikin manyan sharuddan da ake buƙata kafin a fitar da bizar Hajji ga masu niyya.
Alhaji Sa’adu ya ƙara da cewa an kammala duk shirye-shiryen da suka dace tare da shugabancin Asibitin domin tabbatar da cewa aikin zai gudana lafiya ba tare da wata matsala ba.
Ya lura cewa duba lafiyar bana ya fi na shekarun baya zurfi, domin yana kunshe da gwaje-gwaje na mahimman sassan jiki, ciki har da na zuciya, domin tabbatar da cewa duk wanda zai tafi Hajji yana da ƙoshin lafiya.
Shi ma da yake jawabi, Daraktan Lafiya na Asibitin kwarerru na Gombe, Dr. Sambo Dawa, ya tabbatar da cewa dukkanin masu niyyar Hajji za su samu cikakken duba lafiya daga ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Dr. Dawa ya ce asibitin ya tanadi kayan aiki da ma’aikatan da suka dace domin gudanar da aikin yadda ya kamata bisa ka’idojin lafiya na ƙasa da ƙasa.
Wannan duba lafiyar zai taimaka wajen kare lafiyar alhazan jihar Gombe yayin aikin Hajjin 2026.


