Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza
Published: December 3, 2025 at 8:10 PM | By: Bala Hassan | Updated: December 3, 2025

Babban sakataren MDD, Antonio Guterres, yace akwai babban kuskure kan yadda Isra’ila ta gudanar da farmakin soja a zirin Gaza, kuma akwai kwakkwarar shaidar cewa ta aikata laifuffukan yaki a lokacin hare-haren.

Da yake magana yau laraba a wajen wani taron da kamfanin dillancin labarai na Reuters ke shiryawa, Mr. Guterres yace an yi biris baki daya da illar hare-haren a kan fararen hula da kuma lalata muhallansu a fadin Gaza.

Yace Isra’ila ta ce manufarta ita ce ta murkushe Hamas, amma kuma, ba Hamas din aka murkushe ba.

An kashe mutane fiye da dubu 70 a Gaza a lokacin wannan farmaki na Isra’ila, wanda ya biyo bayan harin da Hamas ta kai ta kashe mutane 1200 tare da kama mutane 251 a watan Oktobar 2023.

Da aka tambaye shi ko akwai alamun an aikata laifuffukan yaki a wannan farmaki na Isra’ila, babban sakataren na MDD yace akwai kwararan dalilai na yarda da cewa an aikata hakan.

An kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin tun 10 ga watan Oktoba, amma Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare tare da rushe gine-ginen da take ikirarin cewa cibiyoyin Hamas ne.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a
Next Post: RSF Ta Kasar Sudan, Tana Yin Garkuwa Da Mazauna A Yankin Darfur

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya Labarai
Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna Labarai
Shugaba Trump Ya Bukaci A Cigaba Da Zanga Zanga A Iran Labarai
Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana
  • Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani
  • Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Hukumar NAHCON Ta Kamallah Shirye Shiryen Hajjin 2026 A Kasar Saudiya Labarai
  • Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
  • Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
  • Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai Afrika
  • Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Sojojin Faransa Sun Karyata Zargin Bobi Wine Labarai
  • Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.