Wasu ‘yan sanda kasar Turkiya tare da ‘yan kungiyar ta’addancin ISIS sun rasa rayukan su a wani artabu da aka yi da bindigogi a arewa maso yammacin Turkiya ranar Litinin, a cewar ministan harkokin cikin gida na kasar.
Wannan ya biyo bayan tsare mutane 100 da ake zargin ‘yan kungiyar na ISIS ne, da suke shirin gudanar da hare-hare ranar kirsimeti da kuma ranar sabuwa shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Ali Yerlikaya, ya ce ‘yan sanda 8 tare da wani jami’in tsaro ne suka jikkata a wani samame da aka kai wani gida a garin Yalova, a gabar tekun Marmara dake kudancin Instanbul kuma an kai samame zuwa gidaje fiye da 100 ranar Litinin.
Turkiye ta tsaurara kai farmaki ga ‘yan kungiyar ta’addan a wannan shekara, a yayin da suka sake kunnowa idon duniya.


