Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya
Published: March 28, 2026 at 7:05 AM | By: Nasiru Adamu Elhikaya

APC Ta Yi Babb

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/03/APC-CONVENTION-ENDED-IN-CONSENSUS.mp3

an Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta gudanar da babban taro na kasa inda ta amince da mukaman dukkanin shugabannin jam’iyyar ba hamayya.

Taron dai wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja , ya samu halartar dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga fadin Najeriya.

“Masu sukar cewa mu na neman maida Najeriya kasa mai bin jam’iyya daya ba haka ba ne, don ni na yi amanna da gasa a tsarin dimokradiyya amma hakan bai haramtawa kowa yin hulda da abokan siyasa ko jam’iyyar da ta kwanta ma sa a rai ba” Inji shugaba Tinubu a jawabin da ya gabatar cikin salon jamawninsa na magana daya bayan daya sannu-sannu kwana nesa.

Shugaban wanda ya nuna akwai kwarin guiwar gyaruwar lamura na kuncin tattalin arziki da a ke fuskanta, ya bukaci a yi shiru na minti daya don karrama marigayi shugaba Buhari da wani minti daya don sauran wadanda su ka kirkiro APC amma kuma sun kwanta dama.

Nan take a ka rantsar da shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin Nantawe Yilwatda daga jihar Filato.

Sakataren kudi na jam’iyyar Ambasada Haruna Gimsau ya ce ba sabon abu ba ne daidaitawa wajen fidda shugabannin jam’iyya.

Ita ma mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar Zainab Abubakar wacce ta sauko daga dandalin rantsarwa ta na annashuwa, ta ce hakan kwarin guiwa ne kan babban zabe na 2027.

Shugaba Tinubu ya kare gyara da a ka yi ga dokar zabe ta 2023, ya na mai caccakar ‘yan adawa da cewa ba daidai ba ne su yi korafin kan gyaran.

 

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Mahaifiyar Nasiru El Rufai Ta Rasu
Next Post: Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa

Karin Labarai Masu Alaka

Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika
An Kashe Mutane 7 A Unguwar Dorayi Dake Kano Najeriya
Rundunar ‘Yan Sanda Sun Ceto Wani Daga Hannun Masu Garkuwa Najeriya
Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
Gwamnatin Tarayya Tana Neman Kudi Domin Aiwatar Da Kasafin Kudin 2026 Najeriya
An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tsofin Shugabanin Kasa Sun Karbi Bakoncin Hafsan Sojin Najeriya Tsaro
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan Afrika
  • Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
  • Kamfanin Jiragen Saman Ethiopia Zai Kafa Babban Filin Jirgi Afrika
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
  • Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote Labarai
  • Majami’ar Anglican Zasuyi Taron Zaben Sabon Shugaba Afrika
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.