Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi EFCC da kauce wa ka’idar aikin ta na yaki da cin hanci, yana mai cewa hukumar ta koma “makamin siyasa” da ke farautar ’yan adawa.
A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a Abuja, Atiku ya ce Siyasantar da binciken cin hanci ya lahanta kimar EFCC, yana mai zargin hukumar da zaben wadanda za ta bincika bisa siyasa, ba bisa hujjoji ba.
Ya ce kama tsohon Babban Lauyan Gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), wani bangare ne na bin ’yan adawa cikin son zuciya, yana tuhumar EFCC da zama “reshen APC” da ke kokarin kafa tsarin jam’iyya ɗaya.
Atiku ya nuna cewa EFCC ta tsananta aiki ne bayan jam’iyyar ADC ta karu a matsayin babbar Jam’iyyar adawa, inda ya ambaci matakan da ya ce an dauka kan Malami da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yayin da ake watsi da zarge-zargen da suka shafi magoya bayan gwamnati.
Ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da bai wa wasu tsoffin gwamnoni da ke da shari’o’in cin hanci mukaman gwamnati, yana cewa EFCC ta kasa nuna rashin amincewa.
Atiku ya yi ikirarin cewa da Malami ya koma APC, “da ba za a taba taba shi ba,” yana mai zargin hukumar da amfani da tsoratarwa don tilasta ’yan siyasa shiga jam’iyyar gwamnati.
Ya yi gargadi cewa ba za a samu ingantaccen yaki da cin hanci ba idan aka ci gaba da siyasantar da hukumomi, yana kira ga EFCC ta cire kanta daga tasirin siyasa domin kare mutuncin ta.


