Da yake magana kan matakin soja da Amurka da Isra’ila suka dauka kan Iran, babban sakataren MDD Antonio Gutierrez, yace, “Na yi Allah wadai da fadada matakin soja a gabas ta tsakiya. Amfani da karfin soja da Amurka da Isra’ila suka dauka kan Iran, da martanin da Iran ta mayar a duk fadin yankin, yana zagon kasa ga zaman lafiya da tsaro a duniya.
“Ina kira da a hanzarta tsaida fadan. Kasa yin haka yana iya jefa yankin cikin rikici, wadda zai yi barazana ga farar hula da kuma zaman lafiya a yankin. Ina kira da babban muriya ga duka sassa su gaggauta komawa teburin shawarwari.
A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa, kasashen Jamus, da Faransa, da Britaniya, sunyi Allah wadai da hare haren da Iran take kaiwa, suna masu cewa Farisa ta daina kai hare haren kan mai uwa da wabi.
“Muna sake nanata burin mu na tabbatar da ganin an sami zaman lafiya a yankin, da kuma kare rayukan farar hula,” inji shugaban Faransa Emmanuel Macron, shugaban Jamus Fredrich Merz da PM Britaniya Keir Starmer, suka ce a cikin sanarwar, suka kara da cewa, suna son ganin an koma teburin shawarwari.


