“Sulhu da ‘yan bindiga, Boko Haram, da duk wani dan ta’adda shine mafita a Najeriya” Rt. Hon. Aminu Abdulfatah. (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna).
Mun gani ai yake yake da akeyi a duniya, kamar na Ukraine da Rasha, Falasdin da Izra’il duk yanzu sulhu ake kokarin yi domin asamu mafita.
Don haka ya kamata a fadakar da Fulani asaka su a makarantu domin zama mutane masu muhimmanci a cikin al’ummah. Hakkokin su da aka tauye a basu, a yiwa kowane dan kasa adalci.
An yi a baya mun gani, lokacin da masu tada kayar baya a yankin Neja Delta, sulhu akayi dasu a lokacin Shugaban kasa marigayi Umaru Musa ‘Yar-adua. Aka biya musu bukatun su, aka kaisu makarantu, yanzu ga sunan sun zama manyan mutane, me zai sa baza’a yi ma wadannan ba.
Ya kara da cewar ai tarihi bai manta abu da ya wuce, don kuwa sabon Ministan Janar Christopher Musa, shi ne tsohon hafsan tsaron kasar wanda ya bar mukamin a ‘yan kwanaki, amma matsalar tsaro bata kare ba a kasar lokacin sa. To abun da bai yi a wancan lokacin ba, ya zai iya yin shi a yanzu? Babbar fatar mu dai itace Allah ya bashi ikon yin maganin matsalar, amma dai abu ne mai wuya.
Sau da yawa akan sa siyasa a cikin harkokin tsaro, wanda hakan ba zai haifawa kasar da wani alkhairi ba. Da yawa kuma ana ganin cewar ministan tsaro yana bada umurni ga shugabanin tsaro, ba haka abun yake ba, don kuwa suna da damar ganin shugaban kasa a kowane lokacin.
Shi yasa idan akan ga laifin Badaru to ba’a yi mishi adalci ba. Amma dai koma me ake tunani zamu sa ido don ganin irin rawar da zai taka, wadda bai yi ta ba a lokacin da yake jagoranatar sojojin kasar. Ai sauya suna ko matsayi ba shi ne aiki ba, aiki a zuci ya ke da kuma son kasa, sune abubuwan da zasu taimaka a kawo karshen matsalar.
Akwai bukatar gwamnati ta yi tattaunawa ta massamman da ‘yan ta’addar, aji matsalolin su, a yi sulhu da su, a baiwa kowa hakkin shi don samun zaman lafiya mai dorewa ga al’umar kasa. Kada kuma a manta wasu da yawa suna son a cigaba da wannan yakin don kuwa ta nan suke samun kudi.


