Wasu majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce an kashe sojoji akalla 8, aka raunata wasu 50 a lokacin da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka kai farmaki a kan wani sansanin sojoji dake jihar Borno.
Majiyoyin suka ce ‘yan bindigar na Boko Haram sun isa a kan babura da motoci masu sulke a ranar litinin.
Wata majiyar soja a Najeriya ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wannan sansani an kafa shi ne a wani bangare na farmakin da ake kaiwa da nufin tumbuke ‘yan Boko Haram daga wani yankin da suka lakaba ma suna Timbuktu, wanda yanki ne da ya tashi daga Damboa zuwa Maiduguri, ya yi yamma zuwa Ngamdu, ya sake yin gabas zuwa Damboa.
A wata sanarwar da ta bayar ranar laraba, rundunar sojojin Najeriya ta ce sojoji sun kori ‘yan Boko Haram daga sansanoninsu da dama dake cikin wannan yanki na Timbuktu, suka kuma wargaza shirye-shiryen kai hare-hare da motocin da aka dana bama-bamai cikinsu.
Rundunar ta ce dakaru sun samu nasarar katse hanzarin wata motar da aka shake ta bama-bamai, amma wata a bayanta ta samu halin shigewa cikin inda sojojin suka yi daga ta kashe wasu sojoji da fararen hula masu aikin sa kai, wadanda aka fi sani da suna Civilian-JTF.
Wani dan rundunar Civilian-JTF ya tabbatar da wannan fada da aka gwabza yana mai fadin cewa ‘yan Boko Haram da suka kai harin sun ninka sojojin dake sansanin.
Tuni dai rundunar sojojin ta janye wadannan sojoji zuwa babban sansaninta dake garin Damboa kuma an kwashi gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka ji rauni zuwa asibitin sojojin dake barikin Maimalari a garin Maiduguri.


