Kasar Burkina Faso ta saki jami’an Rundunar Sojin Sama ta Najeriya 11 da aka tsare.
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da sakin wani jirgin saman Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) da kuma jami’ansa 11 da aka tsare a ƙasar Burkina Faso, bayan da jirgin ya yi saukar gaggawa.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Mista Kimiebi Ebienfa, ya sanar da wannan ci gaban a daren Laraba, inda ya ce a taƙaice: “Eh, an sake su.”
Tabbatarwar ta biyo bayan wata ganawa da Ministan Harkokin Waje, Mista Yusuf Tuggar, ya yi da shugaban gwamnatin soji ta Burkina Faso, Mista Ibrahim Traoré, a birnin Ouagadougou.
Tuggar ya jagoranci tawagar Najeriya bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, inda ya yi wa manema labarai bayani kan sakamakon tattaunawar.


