Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Channels TV: Ta Yi Rashin Hazikin Dan Jarida Mr Khani
Published: February 15, 2026 at 8:53 AM | By: Bala Hassan | Updated: February 15, 2026

Daya daga cikin ‘Yan Jarida 13 da sukayi hatsarin Mota a Bauchi ya Rasuwa

Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin ‘Yan Jarida  da sukayi hatsarin Mota a Jihar Bauchi da ke Arewa maso gabas a Najeriya mai suna Khani Ben.

Khani Ben ma’aikacin ne a gidan talabijin na Channels TV ya shahara ta wajan daukar hoto kuma yana wakiltar tashar Channels TV a gidan Gwamnatin Jihar Bauchi.

A ranar Juma’a 6 ga watan Fafurairun 2026 ne tawagar ‘yan Jarida a jihar Bauchi sukayi wani mumunar hatsarin Mota a kan hanyar Yashi zuwa Yelwan Duguri,yayin da zasuje aikin Kaddamar da katafaren Makaranta a garin Yelwan Duguri dake Karamar hukumar Alkaleri a Bauchi wacce hukumar  raya Arewa maso gabas ( NEDC) ta gina.

Ben yana daya daga cikin mutane 14 da hatsarin ya rutsa da su

Tun bayan faruwar lamarin Ben ya samu kansa  cikin mawuyacin hali ganin yana daya daga cikin wadda suka fi samun mumunar rauni sai dai dukkanin su sun samu kulawa daga Gwamnatin Jihar Bauchi da (NEDC) a Babban Asibitin kuyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda anan ne rai yayi halinsa.

Rasuwar Mr Ben ya bar babbar gibi a harkar jarida musamman a kafar watsa labari ta Channels TV da ma gidan Gwamnatin Jihar Bauchi inda yake aiki da kuma abokan aikinsa da sauran ma’abota gidan talabijin na Channel TV.

Mr Khani Ben ya kasance haziki kuma jajurtatce wajan aikin jarida da kuma iya mu’amula da al’uma ya rasu ya bar matarsa ​​da ‘ya’yansa biyu.

“Muna mika ta’aziya wa Iyalai, da ‘yan uwansa da hukumar gudanawa na Channels TV da ‘yan Jaridar jihar Bauchi tare da Gwamnatin Jihar Bauchi bisa wannan Babban rashi. GTA Hausa.

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana
Next Post: Kasar Saudiya Zatayi Gwajin Noman Dabino A Kano

Karin Labarai Masu Alaka

Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Kwankwaso Yayi Kakkausar Lafazi Bayan Ficewar Abba Kabir Yusuf Daga NNPP Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Jihohin Arewaci Sun Kafa Asusun Yaki Da Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sauka A Mukaminsa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojojin Amurka Sun Isa Najeriya Don Yaki Da Ta’addanci Amurka
  • Fafaroma Leo Yayi Allah Wadai Bisa Karuwar Yake Yaken Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Kasashe Biyar Zasu Tura Sojoji Domin Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Gaza Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yarjejeniyar Britaniya Da Mauritius Kan Tsibiran Chagos Cin Zarafi Ne Labarai
  • Jakadan Kasar Sin a Najeriya Ya Ziyarci Tinubu Najeriya
  • IBB: Ba Shakka Abiola Ya Lashe Zaben Yuni 12 Rediyo
  • Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
  • Duniyar Dambe A Makon Jiya Nishadi
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.