Aliko Dangote, shugaban masana’antun kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya zargi Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta (NMDPRA), Farouk Ahmed, da cin hanci, yana mai cewa ya biya dala miliyan 5 a matsayin kuɗin makarantar sakandare ga ’ya’yansa huɗu a ƙasar Switzerland.
Dangote ya yi zargin ne a yayin wani taron manema labarai a Matatar Dangote a ranar Lahadi, inda yace irin wannan kashe kuɗi ya wuce ƙarfin albashin shugaban hukumar, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta binciki lamarin.
Attajirin ya ce ya dace a ba Ahmed damar wanke kansa ta hanyar bincike, ba tare da korar sa ba, amma ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan makarantun Switzerland idan suka musanta zargin.
A wani bangaren kuma, Dangote ya bayyana cewa farashin man fetur zai ragu zuwa kusan naira 740 kowace lita a Lagos daga ranar Talata, bayan da matatar tasa ta rage farashin zuwa naira 699.
Ya ce tashoshin MRS ne za su fara nuna sabon farashin, yana mai jaddada cewa tace man fetur a cikin gida zai amfani ’yan Najeriya duk da asarar da masu shigo da mai za su tafka a Kasar.


