Dogarawan ruwa na Amurka suna dakon isowar karin jami’anta kamin su sake yunkurin shiga wani jirgin dakon mai da suka kama wadda ake zargi yana da alaka da kasar Venezuela da suke binsa tun ranar lahadi, bayan da jirgin yaki amincewa dakarun su shiga jirgin, kamar yadda wani jami’ia da wani da yake da masaniya gameda lamarin ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Jirgin wanda kungiyoyi da suke da masaniya gameda zirga zirga cikin ruwa suka ce sunansa Bella 1, yaki ya amince dogarawan ruwan na Amurka su shiga ciknsa, saboda haka aikin yin haka a dole ya fada kan wasu rundunoni guda biyu na dogarawan ruwan, wadanda suna iya durkowa kan jirgin ruwan daga jirage masu saukar ungulua.
Kwanaki da aka yi ana farautar jirgin ruwan mai dakon mai, ya nuna burin gwamnatin Trump na kama jiragen ruwanda suke da alaka da Venezuela da aka azawa takunkumi, da kuma karancin ma’aikata da kayan aiki da za su aiwatar da kuduri na gwamnati dake Washington.


